Kungiyar Tarayyar Turai (EU) na son fara sayen iskar gas daga Najeriya da nufin rage dogaro da Rasha da kuma martani kan mamayar da Rashar ta yi a Ukraine.
Kasashen EU sun bayyana kudirinsu na fara sayen iskar gas daga Najeriya ne a lokacin da jami’an diflomasiyyar kasashen Turai suka kai ziyara Najeriyar a ranar Litinin.
- Sakacin kasashen Turai ne ya sa har Rasha ta mamaye mu – Shugaban Ukraine
- ’Yan siyasa sun koka da kamun ludayin sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa a lokacin ziyarar, jami’an diflomasiyyar sun samu ganawa da shugabannin kamfanin mai na kasa, inda suka bayyana shirinsu na karfafa alaka da Najeriya da kuma da fara sayen mai da iskar gas daga Najeriya kamar yadda sauran kasashen ketare ke yi.
Jakadan EU a Najeriya Samuela Isopi ya ce, “Matsayinmu ba wai na babbar abokiyar huldar Najeriya ba ne kawai, muna son kulla alaka da ita a bangaren mai da iskar gas, saboda yawancin kamfanonin da ke aiki tare da ku na kasashen Turai ne, saboda haka mu ma muke son zama daya daga cikin abokan huldarku.”
Har ila yau rahoton ya bayyana cewa shugabanin kamfanin NNPC sun tabbatar wa wakilan Turai cewa a shirye kamfanin yake ya kara yawan iskgar gas din da yake fitarwa a kasuwannin duniya.
Da ma dai Najeriya ce kasa ta hudu da ke safarar iskar gas zuwa Turai, inda aka yi kiyasin cewa kusan kashi 40 cikin 100 na gas din da kasar ke fitarwa ana kai shi kasashen Turai ne.