Biyo bayan tarar Naira miliyan biyar da Hukumar da ke Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta ci gidan talabijin na Trust TV saboda yin rahoton binciken kwakwaf kan ayyukan ’yan bindiga, gidan Talabijin din ya ce don al’umma ya yi rahoton.
Gidan talabijin din dai daya ne daga cikin kafafen yada labarai mallakin kamfanin Media Trust, mamallaka jaridun Daily Trust da Aminiya.
- Buhari zai jinginar da tashar jiragen ruwa ta Badagry da ke Legas kan Naira tiriliyan 1
- An hana ’yan wasa ‘durkusa gwiwoyi a kasa’ kafin fara wasanni a gasar Firimiya
Tarar dai da hukumar ta NBC ta sanya wa gidan Talabijin din ta ce saboda rahoton ya saba wa Kundin Watsa Shirye-shirye na Kasa ne.
Cikin wata sanarwa da hukumar gudanarwar kamfanin Media Trust ta fitar, ta bayyana cewa a matsayinsu na gidan Talabijin a Najeriya, sun watsa shirin ne domin haskawa al’umma tirka-tirkar da ke cikin lamarin ‘yan ta’adda a kasar nan, da kuma yadda hakan ke shafar miliyoyin al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba.
Hukumar ta kuma ce a matsayinta na gidan talabijin, tana fifita bukatun al’umma ne ta hanyar fallasa ayyukan ’yan bindigar da ya addabi miliyoyin ’yan Najeriya.
“Rahoton ya bi diddigin matsalar tsaron ne tun daga tushe, wacce bisa ga dukkan alamu yanzu take kokarin gagarar Kundila.
“Ya bankado yadda batutuwa irinsu rashin adalci, kabilanci da raunin shugabanci suka rura wutar rikicin”.
Bai tsaya a nan ba sai da ya tattauna da kwararru da ma mahukunta a Najeriya da nufin lalubo bakin zaren, cikinsu har da Minista Lai Mohammed da Sanata Sa’idu Dansadau, wanda ya fito daga Zamfara, jihar da rikicin ya fi kassarawa.
“Rahoton ya kuma fallasa mawuyacin halin da mutanen da rikicin ya shafa suke ciki,” inji sanarwar.