Gwamantin kasar Tanzania za ta sake haramta shigo da ‘yan tsaki sabbin kyankyasa daga waje.
Gwamnatin ta ce haramcin shigo da kajin sabbin kyankyasa zai fara ne daga mako mai zuwa.
- Jama’a su hanzarta su yi rajistar katin zabe —Sarkin Kano
- Fargabar kai hari ta sa dalibai zana jarrabawa 13 a yini guda a Abuja
A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce za ta yi hakan ne domin kare masu sana’ar kyankyasar kaji na cikin gida.
Hakan kuma a cewarta, zai hana shigo da ‘ya ‘yan tsaki marasa inganci daga ketare.
A cewar sanarwar da Ma’aikatar Kula da Dabbobi da Kiwon Kifi ta Kasar ta fitar, ta ce, manufar wannan hanin shi ne ya inganta kasuwar samar da kaji na cikin gida.
Mataimakin Minista a Ma’aikatar Kula da Dabbobi da Kiwon Kifi, Abdallah Ulega ya ce, gwamnati ba za ta sake bayar da izinin shigo da ‘yan tsaki daga ketare ba daga ranar Asabar mai zuwa.
Wannan dai na zuwa ne bayan wata ganawa da aka yi tsakanin Ma’aikatar da masu ruwa da tsaki a Dadoma, babban brinin kasar.
Masu sana’ar kyankyasar kaji sun yi Allah wadai da karuwar fasa kwaurin ‘yan tsaki daga waje, wadanda ake sayar da su a farashi kasa da wanda ake kyankyashewa a cikin gida.