✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tanko Yakasai na fafutikar kare Arewa

Edita ka ba ni dama in yi tsokaci kan Babbar kungiyar masu akidar NEPU da PRP  a  Masarautar Kazaure da ta shiga jerin dubban ’yan…

Edita ka ba ni dama in yi tsokaci kan Babbar kungiyar masu akidar NEPU da PRP  a  Masarautar Kazaure da ta shiga jerin dubban ’yan kasa da suke yaba wa gagarumar guddumawa da ubanmu, mai girma Alhaji Tanko Yakasai ya bayar wajen neman ’yancin Najeriya. Babu shakka mai girma Alhaji Tanko Yakasai a matsayinsa na sakataren Jam’iyyar NEPU, kuma na hannun daman Malam Aminu Kano ya sha gwagwarmaya.  Don ya fi son dan Arewa ya hau mulkin kasar. Ya yi wa Shehu Shagari mai bayar da shawara. Yana ci gaba da fafutikarsa a kungiyar Dattawan Arewa.
Daga Malam Sani Mai Rediyo, Kazaure.

Sakonnin waya

Godiya ga Akun Bulama
Edita muna gode wa Akun Bulama. Saboda yadda yake tsage gaskiya a siyasar Najeriya, ba tsoro. Allah Ya bai wa aku zuriya ta gari. Daga Ali Fancy Garko 08171748500.

Ina labaran Jihar Bauchi?
Edita sannu da aiki, don Allah ka ba ni dama in mika kokena. Wakilinku na Bauchi kullum ba shi da wani labari sai na ma’aikatar lafiya za ta yi feshin sauro. Daga Alhaji Musa Mai Bulawus, Kasuwar Wunti, Jihar Bauchi 08087238966

Ga Mukhtari Shagari
Edita, ka ba ni dama in yi kira ga mataimakin Gwmanan Jihar Sakkwato, Alhaji Mukhtari Shagari da ya amsa kiran sakkwatawa, ya fito takarar gwamna a shekarar 2015. Daga Bello Dandin Mahe Suleja. 08055975622.

Jinjina ga Janar Buhari
Salam, Aminiya don Allah ku isar min da sakon jinjina ga gwarzon namiji, Janar Muhamamdu Buhari. Daga Isma’il Alkyabba Funtuwa 07039495283.

A yi zaben kananan hukumomi a Katsina
Assalamu alaikum. Muna kira ga gwamnatin Jihar Katsina da ta taimaka ta yi zaben ciyamomi, don su samu damar yi wa mutane aiki. Daga Abubakar Abdullahi danja 08051218705.

Ga Aminiya
Gaisuwa ga ma’aikatan Aminiya, kana ga cigiyata. Ina Adam A. zango? Daga Abdul dan Katsinawa 08168722855.

Taron Jonathan
Assalamu alaikum Aminiya, ina son yin tsokaci game da taron da Jonathan ya kira na kasa, to ya sani mu ’yan Najeriya fa kanmu a hade yake. Burinmu a yi zaben gaskiya a 2015, shi ne abin da zai hada kan Najeriya. Daga Mahmud Harisu Jalingo 08112170184.

Ga Manjo Al-Mustapha
Muna son Al-Mustapha ya karasa shekarunsa na ritaya a gidan soja. Daga Ibrahim Jigawa 08037425125.

Ga Gwamna Shema
Salam. Don Allah Gwamna Shema ka biya daliban Jihar Katsina kudin tallafin karatu, wato “scholarship,” na 2013/2014. Don dalibai na cikin wani hali. Daga Rabi’u B. Lawal Funtuwa 08153171016.

Muna neman shugaba nagari
Shugaba Jonathan kada ka manta da 2015, mu talakawa muna neman shugaba nagari. Daga Usman Bala Kagoro. 07037084451.

Ga Gwmanatin Neja
Gwamnatin Neja, an bar jaki, ana ta bugun taiki. Ana ta bin masu talla da sojoji da ’yan sanda da Cibil Defence, suna kamasu, ana kai su  kurkuku, don suna neman abin da za su ci. Gwamantin Neja ki sake tunani a irin wannan lokacin da ake ciki na rashin tsaro. Daga danliti Pillars, R/Kebe Kano/Dei-Dei, Abuja 07037874889.

A feshe mana sauron Kano
Edita, don Allah a yi kira a Gwamnatin Kano, a dawo da feshin maganin sauro, saboda malaria tana damun jama’ar jihar. Daga Hafizu Sabi’u danladi Gama C, Kwanar JAba 08066551855.

Murnar ’yancin kai
Ina yi wa duk ’yan Najeriya murnar cika sheka 53 da smaun ’yancin kan dunkulalliyar kasata Najeriya, musamman iyayena Alhaji Lawal Kaita da Yahaya dan uwa, Shugaban PDP na karamar Hukumar Bakori da ma’aiaktan Aminiya. Allah Ya kara mana kaunar juna da kishin kasa. Allah Ya kara wa Shugabanni tausayi; Allah Ya kara wa talakawa hakuri. Daga Amiru Isa Bakori 080759599086.

Ga Farfesa Jega
Edita, ka yi hakuri da sakona ga Farfesa Attahiru Jega. Duk halin da Najeriya ta shiga kai ne sila. Don Allah ka yi zaben gaskiya 2015 don ka samu albarkar talakawa. Daga Anas A Lawal Mai’aduwa, Jihar Katsina. 08056071723.

kokon bara ga Aminiya
Editan Aminiya, ina mika kokon barata da ka sanya ni cikin masoya wannan jarida taku mai albarka da kuma farin jini. Allah Ya kara daukaka ku. Amin. Daga Khadija Chindo 08057516675.
A kara kwafin Aminiya
Salam Aminiya Hausa. Don Allah Edita ka mika kokena ga hukumar da abin ya shafa. A kara mana yawan adadin kwafin Aminiya Hausa. Mu a nan Legas. Domin kuwa wannan Aminiya Hausa ta samu karbuwa a nan bangaranmu. Saboda farin jininta ga mu mazaunan Legas. Wassalam. Daga Alhaji danladi kofa Kasuwar Mile 12, Legas. 07035699758.

Muna nan a PDP
Muna nan a PDP, kuma Shugaban kasa Goodluck Jonathan Allah Ya saka ma da alkhairi, domin ba laifinsa ba ne. Saboda PDP ta rabu biyu. Me suke so su yi? Daga Ya’u Isiyaku Kano Sumaila 07035541541.
Ga ’yan PDP
Zuwa ga ’ya’yan PDP a Najeriya ba kuma fara shiga tatsuniya ba, yanzu kuka fara rikicewa. Mu dai talakawan Najeriya sai dai murna, karshen mulkinku ya zo. Daga U.S Shyman, Jihar Kebbi 07061584114.

Muna tare da Jonathan
Sabuwar jam’iyyar PDP ba za ku kai labara ba, PDP sak. Ba wata sabuwar PDP, muna tare da Jonathan Goodluck Ebele mai nasara 2015. Sai Jonathan. Daga Auwalu Musa Ibrahim Warure, Gwale, Jihar Kano. 08066885356.

Jinjina ga Sarkin Dass
Allah Ya kara wa Mai martaba Sarkin Dass, Dokta Usman Bilyaminu Lafiya. Allah Ya jikan Baba. Daga Isa Garba Waziri Burgel. 07037733411.