✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tankar mai ta yi bindiga a Legas

Tankar man ta yi hatsari sannan ta kama da wuta a cikin dare.

Wata tanka dauke da litar man fetur dubu 45 ta yi hatsari sannan ta kama da wuta a yankin Egbeda na Jihar Legas.

Jami’in Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) a yankin Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) faruwar hadarin.

Ya ce da misalin karfe 12:20 na daren Talata hukumar ta samu labarin cewa tankar man ta kama da wuta a yankin Abule Ado cikin Karamar Hukumar Amuwo Odofin, lamarin da ya jefa mazauna cikin zullumi.

Ya ce NEMA da hadin gwiwar takwararta ta Jihar Legas sun bazama zuwa wajen da lamarin ya faru domin bayar da dauki da tabbatar da tsaron lafiyar jama’a. 

Sai dai ya ce: “Ba a samu hasarar rai ko barnar wata dukiya ko guda ba.”