✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tanka cike da man dizal ta kama da wuta a Legas

A safiyar yau Litinin wata tankar mai da ta dauko man dizal da ya kai lita dubu 33 ta kama da wuta a unguwar Ayobo…

A safiyar yau Litinin wata tankar mai da ta dauko man dizal da ya kai lita dubu 33 ta kama da wuta a unguwar Ayobo da ke  jihar Legas.

Wutar ta kama tankar ne a cikin rukunin gidajen Abesan da ke hanyar Ipaja Karamar Hukumar Alimosho  ta Legas. Ana zargin wutar ta tashi ne lokacin da ake iban man daga cikin bututun tankar.

Mazauna unguwar ne suka sanar da jami’an Hukumar masu bada agajin gaggawa ta Legas (LNSC) daga bisani suka sanarwa Hukumar kashe gobara ta jihar.