Kananan yara akalla 81 sun rasu daga cikin yara 5,200 cutar tamowa ta rashin abinci mai gina jiki ta kwantar a asibitoci a Jihar Nasarawa.
Hakan ta faru ne a cikin wata takwas da suka gabata a kananan hukumomi 13 na Jihar Nasarawa, a cewar Babbar Jami’ar kula da abinci mai gina jiki ta Jihar, Halima Yusuf, ta bayyana.
- ‘Na ci karo da maciji a ganyen latas da saya’
- An haifi jariri da azzakari uku
- Dan majalisa ya halarci zaman Majalisa tsirara
- ’Yan sa-kai sun aika ’yan bindiga lahira a Kasuwar Dansadau
Ta shaida wa taron wayar da kai kan abinci mai gina jiki cewa “Kananan yara 81 sun rasu daga cikin yaran da aka kwantar a asibitoci a jihar, wasu 2,000 kuma sun murmure.”
Shugaban Kwamitin Abinci Mai Gina Jiki na Jihar, Osama Abdul, ya ce kwamitin ya bullo da hanyoyin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki, wadanda ake sa ran kashe wa Naira biliyan uku.
Tun da farko Babbar Sakataren kungiyar samar da abinci mai gina jiki a a Najeriya CS-SUNN, Beatrice Eluaka, ta bayyana damuwa game da yawaitar matsalar karancin abinci mai gina jiki a jihar ta Nasarawa.
Ta jaddada muhimmancin Gwamnatin Jihar ta bullo da hanyoyi na cikin gida domin magance matsalar.