✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambuwal ya lashe kujerar Sanatan Sakkwato ta Kudu

Tambuwal ya bai wa abokin karawarsa tazarar kuri’u 4,976.

Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal ya lashe zaben kujerar Sanatan Sakkwato ta Kudu da tazarar kuri’a 4,976.

Tambuwal ya doke abokin karawarsa kuma sanata mai ci, Ibrahim Danbaba Dambuwa na jam’iyyar APC.

Da yake sanar da sakamakon, Baturen Zaben, Farfesa Abubakar Bagudu, ya ce Tambuwal shi ya zama zakara a zaben bayan samun kuri’u 100,860.

Kazalika, ya ce Dambuwa wanda ya zo na biyu ya samu kuri’u 95,884.