✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyi da tsokacin masu karatu (1)

Matashiya A wannan mako ya kamata mu ci gaba da kasidun da muka faro ne kafin baiwa Malam Tukur Fage makonni biyu da suka gabata,…

Matashiya

A wannan mako ya kamata mu ci gaba da kasidun da muka faro ne kafin baiwa Malam Tukur Fage makonni biyu da suka gabata, amma kwatsam tafiya ta kama ni. Don haka na zakulo wasu daga cikin tambayoyi da tsokacinku, don amsawa iya gwargwado. Idan Allah Ya kaimu mako mai zuwa muna nan tafe da ci gaban fassarar makalar Stebe Dent dake bayani kan motoci masu amfani da makamashin lantarki, da kuma ci gaban kasidar Whatsapp. A ci gaba da kasancewa tare damu.

Tambayata ita ce, don Allah Malam yaya ake yi link din shafi a Facebook ta yadda idan ka yi za ka ga an sa “Continue Reading…”? Daga: Abubakar Sadeek Jibrin Isa
Malam Abubakar barka da warhaka. Wannan rariyar likau (Link) da kake magana a kai kuma wanda kake gani a rubutun wasu a duk sadda suka rubuta a shafinsu, ba su ba ne suke sa wa. Daga tsarin dandanlin ne. Kuma irin wannan na samuwa ne a duk sadda ka yi rubutu mai tsawo, da zarar ka tura shi a zauren shafinka (Wall), za a bayyana kadan ne daga farkon rubutun ko sakon ko kasidar, sauran kuma sai a boye, a rubuta: “Continue Reading….” Duk wanda ya gani ya san ba iyakar rubutun ba kenan, akwai saura a kasa. Hikimar wannan ita ce takaitawa, tare da baiwa mutane ko kai kanka damar ganin wasu sakonnin da ke jerin shafin. Domin idan aka bar sakon da ka rubuta da tsawonsa, to a karshenta yana iya lakume sauran filin da ke shafin, ka kasa ganin sakonnin abokananka, ko naka ma, a takaice.
Bayan haka, wannan ba ya nuna cewa ba za ka iya sa rariyar likau a shafinka ba. Misali idan ka rubuta sako, sai ya zama kana son yin ishara ga wani shafi da kake son masu karatunka su kai gare shi don neman karin bayani, ko a matsayin shaida ga abin da kake son tabbatarwa, to, kana iya kwafo adireshin shafin daga inda yake a Intanet, sai ka zuba shi a daidai inda kake son ya bayyana a shafinka. Nan take akwai manhaja da za ta fahimci abin da ka zuba, sai ta nakalto kadan daga cikin suna ko taken kasida ko hoton da ke cikin wancan gidan yanar sadarwa da ka nakalto adireshinsa zuwa shafinka. Wannan zai baiwa masu karatu ganin kadan daga cikin abin da ke shafin, tare da bayyana adireshin, kamar yadda ka sa. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, don Allah yaya ake “Unlocking” HTC E19, ba tare da amfani da manhajar kwamfuta ba? Daga: Abdallah Abubakar Zakka
Wa alaikumus salam, Malam Abdallah barka dai. Idan na fahimci tambayarka, kamar kana son sanin hanyar bude waya nau’in HTC E19 ce, wacce ta kulle sanadiyyar matsalolin tsawo ko makamantan haka. Yana da kyau mu san cewa kusan dukkan wayoyin salula da ake kerawa a halin yanzu suna da hanyoyin tsawo da kari (Security) don baiwa mai amfani da su aminci da kariya ga bayanai da kuma sirrinsa baki daya. Wadannan hanyoyi sun hada da amfani da kalmomin sirri (Password/PIN cord), da amfani da Zanen kariya (Pattern Cord), musamman ga wayoyi masu dauke da babbar manhajar Android. Idan ka farkar (actibate) da wadannan hanyoyin kariya, a duk sadda ba ka amfani da wayar, za ta kulle kanta. Idan ka tashi amfani da ita kuma sai ka bi hanyoyin bude ta (Unlocking).
Idan ka mance hanyar bude wayar, har ka yi ta gwadawa akai akai, nan take za ta kulle kanta, ta hana ka damar shigar da kalmomin budewa ma karankaf! Hakan kan faru ne idan ka yi ta gwaji sama da iyakar da masu kera wayar suka bat a umarnin karba. A yanayi irin wannan, dayan hanyoyi biyu ne kawai za su cece ka; ko dai ya zama ka tuna adireshin Imel din da ka tsara wayar da shi, tare da kalmomin sirrin Imel din, wato Password kenan. Domin a duk sadda ta kulle kanta, za ta sanar da kai ne cewa, muddin da gaske kaine mai wannan wayar, to ka shigar da adireshin Imel din da ka tsara ta da shi. Idan ka sa, sai a sake bukatar Kalmar sirrin Imel din da ka tsara ta da ita. Da zarar ka shigar shikenan, sai wayar ta bude. Amma idan ka kasa shigar mata da wadannan bayanai, ta kulle kenan har abada! To yaya za a yi? Sai mataki na biyu.
A yadda aka tsara wayoyin salula masu shiga yanayi irin wannan, in har ka kasa tuno adireshin Imel da Kalmar sirrin Imel don bude ta, gani suke kamar kana neman isa ga bayanan dake wayar ne ta haramtacciyar hanya; ma’ana ba kai bane mai wayar; bakon haure ne kai. Shi ya sa za ta kulle; ba sani ba sabo. To amma su masu kera wayar sun san cewa dan Adam na da dabi’ar mantuwa. Ba abin mamaki bane idan mutum ya mance dukkan wadannan bayanai, kuma idan ma ya rubuta su, watakila ya mance inda ya ajiye takardar. Don haka suka samar da hanyoyi guda biyu; hanyar farko ita ce ta yin amfani da wasu isharori (Unlocking Cords) don bude wayoyin salula. Ko dai ta hanyar shigar mata su kai tsaye, ko ta hanyar amfani da manhajar kwamfuta (wanda kace ba ka so) don bude ta. Sai dai ba kowace waya ce ke iya ba ka damar shigar mata da rubutu ba idan ta yi fushi ta kulle kanta. Sannan idan za ta ba ka dama, to, wadannan isharori sun bambanta daga wannan kamfanin waya zuwa wancan. Sannan ga wayoyin da aka kera su a kamfani daya ma, kowace nau’i (Model) da irin nata. Ka ga akwai matsala a nan. Musamman ganin cewa kamfanonin waya ba su raka wadannan wayoyin salula tare da wadannan isharori a yayin da ake kai su kasuwa don sayarwa. A yanayin irin wannan babu wata hanya sai hanyar karshe, wacce ke dauke da hadari ga wayar ita kanta, ko bayanan da ke cikinta, musamman idan wanda zai yi amfani da hanyar bai kware ba.
Hanyar karshe ita ce tsarin da ake kira “Hard Reset”, wato yin amfani da maballan wayar da ke jikinta, don sumar da ita, tare da goge dukkan abin da ke cikinta na bayanai, ta koma kamar yadda aka kero ta a karon farko. Wannan hasashe da natijar da hasashen ke samarwa sun ta’allaka ne kacokam idan aka bi hanyar yadda aka tsara. Amma idan aka yi kuskure, to, wayar na iya macewa gaba daya. Wannan hanyar kuwa ita ce: (1) A tabbata akwai cikakken caji. Idan babu, a mata caji har ta cika. (2) A kashe wayar idan a kunne take. (3) A sake kunna ta, ta hanyar rike maballin kunnawa (On/Off Button) tare da maballin kara sauti (bolume +) a lokaci guda, har sai shafin wayar ya kawo wuta ya fara haske, nan take sai a saki maballan biyu a lokaci guda. (4) In har an yi daidai, wannan zai jefa wayar cikin wani yanayi mai suna “Recobery Mode” ko wani abu makamancin haka; ya danganci kamfanin waya. (5) Idan ya samu kansa a wannan shafi, zai ga zabi kala-kala, ko dai ya ga “Hard Reset” ko “Factory Reset” ko “Reset Phone” tare da “Recober from Back-up” musamman idan wayar HTC ce. (6) Idan wayar mai shafaffen fuska ce (Touchscreen) sai ya yi amfani da maballin kara sauti (bolume up ko bolume +) don gangara ko haurawa don zabar zabin da ya dace da shi. Idan kuma mai maballi ne ba matsala kenan. (7) Idan ya zabi “Hard Reset” misali, sai ya yi amfani da maballin kara sauti har wa yau, don amincewa (wato “Ok” kenan). Domin ko da wayar mai shafaffen fuska ce, idan ta shiga yanayi irin wannan ba abin da ke amfani fuskar don ka shafa da tafin hannunka. Sai a kiyaye. Da zarar ka zabi “Hard Reset” misali, sauran aikin sai ka bar mata. Da kanta za ta sarrafa kanta. Za ta kashe kanta. Sannan ta sake kunna kanta. Hakan zai dauki lokaci; ya danganci nau’in wayar, da yawan bayanan da ke cikinta, sannan da girman mizaninta. Shi ya sa na ce dole a tanadi caji kafin a fara, domin idan tana cikin wannan yanayi caji ya kare, akwai matsala. Ba sai na gaya maka abin da zai faru ba. Wannan shi ne kadan daga cikin abin da na sani, wanda zan iya fada. Allah Ya sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina maka jinjina ta ban girma da yaba wa game da yadda kake wayar da kan al’umma ta hanyoyin sadarwa daban-daban kan fannonin da suka shafi kwamfuta da wayoyin salula. Allah Ya saka maka da alkhairi, ya kuma jikan iyaye. Sakamakon yadda kake wayar da kan jama’a akan wannan ilimi, wannan ya b ani sha’awa matuka, ya kuma sa ni kwadayin wannan harka taka, musamman a irin wannan zamani. Sai dai ban san ko kana da makaranta ta koyar da wannan sana’a ba. Idan akwai, to don Allah a yi mini bayani; da kudinta da dokokinta. In kuma babu, to ina rokonka da ka taimaka min in koyi wannan ilimi a wajenka. Don koyon ilimi a hannun wanda ya goge irinka yana da matukar amfani ga dalibi me neman wannan ilimi. Allah Ya saka da alkhari. Daga: Bukhari M. Barau
Wa alaikumus salam Malam Bukhari, da fatan kana lafiya. Ina godiya matuka da wadannan addu’o’i naka, tare da kyautata zato da kake mini kan kwarewa, duk da cewa na san iya haddin kokarina bai kai haka ba. Allah saka maka da alheri amin. Dangane da ko ina da makaranta, amsar ita ce: a’a. Har yanzu ban assasa wata cibiya don gudanar da ire-iren wadannan al’amura ba, sai dai nan gaba. Akwai wani wannan kuduri mai karfi in Allah ya so. Amma, a tare da rashin sanin inda kake zaune, akwai makarantar Malam Salisu Webmaster da ke Kaduna a Unguwar Sunusi. Akwai cibiya ta musamman da aka dade ana horar da matsanmu kan wannan fanni mai albarka, tare da samun shedar karatu mai inganci, bayan kwarewa a aikace. In har an dace kana kusa da nan, kana iya tuntuba ta don karin bayani. Allah sa mu dace baki daya, amin.

Assalaamu Alaikum, tambayata ita ce: wai yaya ake aiki da “serbice” din blackberry zuwa kwamfuta. Misali, ka hada serbice din blackberry ya rika aiki a kwamfuta ko Wi-Fi ne ko USB. Na gode. Daga Tasi’u Ali G/Dutse
Wa alaikumus salam Malam Tasi’u, da fatan kana lafiya. Idan na fahimceka, kana son amfani da wayar Blackberry ne ta hanyar kwamfutarka; da dukkan hanyoyin sadarwa da ke tare da ita. Idan kana bukatar amfani da wayar Blackberry ta kwamfuta sai ka saukar da manhajar Blackberry wadda ta dace da nau’in wayarka. Idan sabuwar babbar manhajar Blackberry take amfani da shi sai ka saukar da BB10 Blackberry Desktop App. Idan kuma tsohuwar babbar manhajar ce irin su BB5, 6, ko 7 a misali, sai ka saukar manhajar BB7 Blackberry App. Za ka samu wannan manhaja ce a shafin yanar sadarwar kamfanin Blackberry dake www.blackberry.com. Idan ka gama saukarwa sai ka loda mata, wato “Install” kenan. Sai ka jona wayar da kwamfutarka, don su hada alaka da juna. A jikin wannan manhaja da ka loda mata ne za ka dukkan abubuwan da za ka iya aiwatarwa da wayar ta hanyar kwamfutarka, cikin sauki. Daga ciki, za ka iya amfani da wayarka a matsayin makalutun sadarwa ta Intanet. Wato wayar ta zama ita ce mai ba ka yanayin sadarwar Intanet a kwamfutarka. Amma hakan fa ya danganci ingancin sadarwar kamfanin wayar da kake amfani da SIM dinsu ne, da kuma yawan data da ke wayar. Idan babu data a layinka, ba za ka iya aiwatar da duk wani abu da ya shafi Intanet ba, sai dai musayar bayanai tsakanin wayar da kwamfutarka ko akasin hakan. Da fatan ka gamsu.