✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyi da amsoshi kan kimiyya da kere-kere (5)

A bangaren gina manhajar wayar salula (Mobile Applications) kuma, yaren Jaba ya yi fintinkau, a halin yanzu. Domin kusan dukan ko galibin manhajojin wayar salula…

A bangaren gina manhajar wayar salula (Mobile Applications) kuma, yaren Jaba ya yi fintinkau, a halin yanzu. Domin kusan dukan ko galibin manhajojin wayar salula na Android, duk da yaren Jaba ake gina su. A nasa bangare, yaren Python na da tsarin “Kiby” da ake amfani da shi wajen gina manhajar Androids na wayar salula, amma bai shahara ba sosai. Bayan shi kuma akwai tsarin “React Natibe”, wanda bangaren tsarin “React” ne na kamfanin Facebook, mai asali daga yaren “JabaScript”, da ake amfani da shi wajen gina manhajojin wayar salula na Android da na iOS.

Wannan, a takaicen takaitawa, shi ne kadan daga cikin abin da ya samu na alaka da kuma bambancin dake tsakanin yaren Jaba da Python. Da fatan ka gamsu.

 

Assalamu alaikum Baban Sadik, sunana Aliyu Tahir, amma akan kira ni da “Dct Alikson.” Tambayata a nan ita ce: wai shafin nan yana aiki kuwa? Saboda a kullum ina yawan ziyartarsa amma ba na ganin sababbin kasidu, musamman na wannan shekarar, ko me ya sa? Sai na ji daga gare ka. Naka kullum: [email protected]

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aliyu. Lallai shafin yana aiki, kuma ana loda sababbin kasidun da ake bugawa a shafin AMINIYA.  Idan kana son ganin sababbin kasidu da zarar ka hau shafin, bangaren farko daga can sama kurya, za ka ga sababbin kasidu suna yin zarya daga dama zuwa hagu. Bayan haka, da zarar ka gangaro inda jerin kasidu suke masu dauke da tambarin hotunansu, duk kasidar da ka gani tana zarya (Sliding) daga dama zuwa hagu dauke da hotuna, to, duk sababbin kasidu ne.  

Sai dai kuma, kasancewar wannan shafi da ke AMINIYA a duk mako yake bayyana, wannan ya sa ba za a ga wata sabuwar kasida ba sai bayan mako. Duk da cewa ina sa ran bude wani shafi na musamman don karantar da wasu nau’ukan ilimi kan fannin sadarwa a matsayin makaranta, wanda hakan zai ba da damar samun bayanai sababbi a kai -a kai, sai dai a yanzu wannan tsari ne ke gudanuwa.

Kuma idan ba ka mance ba, kusan wata biyu zuwa uku da suka gabata muna ta amsa tambayoyi ne. Wannan ya sa dukan sababbin kasidun na tambayoyi ne da amsa, kamar yadda za ka gani. Da fatan ka gamsu kuma na gode.


Assalamu alaikum, ina fatan kana lafiya. Shin ko kana da makarantar koyar da ilimin kwamfuta ce? Na gode. Ni ne: Alhassan Beli, karamar Hukumar Shira, Jihar Bauchi: Imel: [email protected] 

Wa alaikumus salam Malam Alhassan, a halin yanzu ba ni da makaranta a zahiri na karantar da wannan ilimi, sai dai nan kusa cikin dacewar Allah ina sa ran samar da makaranta ta Intanet don aiwatar da hakan. Idan lokaci ya yi zan sanar in Allah Ya so. Na gode matuka kuma Allah saka da alheri, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, sunana Hassan Muh’d Hassan Daurawa, Kano. Don Allah kasidun Farfesa Abdallah Uba Adamu wadanda ya yi kan ICT muke neman alfarmar in an samu lokaci a turo mana, don mu karanta mu amfana. Mun gode: Hassan Muh’d Hassan: [email protected] 

Wa alaikumus salam Malam Hassan, barka dai. Kana iya duba akwatin Imel dinka don daukar wannan kasida. kasida ce guda daya wacce ya yi mai taken: “Hausa and Information Communications Technologies (ICTs),” kuma ya gabatar da kasidar ce a shekarar 2004. Bayan haka, kasidar na dauke ne da wasu haruffa na Hausa masu lankwasa, wadanda ke bukatar manhajar harafi na musamman kafin su bayyana. Farfesa Abdallah ya samar da wannan manhaja wanda sai ka yi amfani da ita kafin ka gan su. Na hada maka da manhajar (mai suna: “abdallah.ttf”).  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, muna godiya da fatan alheri gare ka. Wai me ya sa ba a ganin kasidu kamar kashi na (1), da na (2), da na (3), sai dai na (4), ko na (8), ko na (9)?  Me ya sa ba a ganinsu a jere?  Na gode. Usman Mu’azu: [email protected]

Wa alaikumus salam, Malam Usman barka dai. Ina kyautata zaton kana nufin a Taskar Baban Sadik (www.babansadik.com) ne. Hakan ya faru ne saboda kasidun karshe ne ke zama a sama, duk wanda ya zo sai fara da su. Idan kana bukatar ganin sauran, a kasan kowace kasida, za ka ga wacce ta gabace ta a bangaren hagu. A bangaren dama kuma za ka ga taken wacce ke zuwa bayan wacce ka karanta.

Misali, idan ka karanta kashi na (3) ne, kana zuwa kasan kasidar, za ka ga wacce ta gabace ta mai lamba ta (2) a bangaren hagu, sannan da wacce ke zuwa bayanta mai lamta ta (4), in akwai ke nan. In kuma ita ce ta karshe a bangaren, to, za ka ci karo da wani sabon maudu’i ne.

Har wa yau, idan kana son ganin dukan kasidun da wani bangare ya kunsa gaba daya, ka gangara kasan shafin gaba daya, za ka ga dukan bangarorin. Sai ka bi wanda kake so. Za ka ga dukan kasidun da ke karkashinsa. Da fatan ka gamsu. Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Ina yi maka fatan alheri da fatan Allah Ya kara basira, amin. Sako daga dalibinka: Idris Ghali Abdu, Bichi Kano: [email protected] 

Wa alaikumus salam, Malam Idris barka dai. Ina godiya matuka da wannan sako naka na fatan alheri. Allah saka maka da mafificin alheri, Ya kuma inganta rayuwarmu baki daya. Na gode matuka.


Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya gida da ayyuka? A gaskiya babu kalaman da za mu iya gode maka da su sai dai mu ce Allah Ya saka da alheri, amin. Na kasance ina bibiyan shafinka da kuma kasidunka a AMINIYA tsawon shekaru. Don Allah ina da tambaya: shin, mene ne (Aliens)? Sannan mene ne amfaninsu? Sako daga Almustapha M. Aliyu, Birnin Kebbi. Almustapha [email protected] 

Wa alaikumus salam Malam Mustapha. Da fatan kana cikin koshin lafiya, amin. Da farko dai tukun, kalmar “Alien” a asalin lugga na Ingilishi, na ishara ne ga wani abu bako, wanda ba a san shi ba. A harshen malaman kimiyyar wannan zamani kuma, musamman na kasar Amurka, kalmar na ishara ce ga wasu bakin halittu da ake ikirarin ana ganin wulkitawarsu a wannan duniya tamu, wadanda kuma, a cewar wadansu, yanayin bai yi kama da na halittun wannan duniya da muke rayuwa a ciki ba.

Misali, akwai hotunan bidiyo birjik da ke yawo a Intanet, musamman a youtube, masu dauke da ire-iren wadannan halittu, a cewar masu loda bidiyon, wadanda suka shigo wannan duniya tamu. Ko kuma suke wannan duniya tamu amma ba a san daga ina suke zuwa ba, masu wulkitawa a sasannin sararin samaniyar wannan duniya tamu.

A jumlace, wadannan halittu da ake kira: “Aliens,” an kira su da wannan suna ne saboda ba a san wasu irin halittu ba ne. Suna cikin jerin abubuwan da ake ganin suna wulkitawa a wannan duniya ba tare da sanin hakikaninsu ba. Malaman kimiyyar sararin samaniya da kimiyyar halittu na kiran su: “Unidentified Flying Objects” ko “UFO” a gajarce. Ma’ana, abubuwa masu wulkitawa da ba a san hakikaninsu ba.

Bayani kan “Aliens” abu ne mai cike da rudani. Wadansu sun ce tabbas halittu ne da ke shigowa wannan duniya tamu daga wasu duniyoyin. Wadansu kuma suka ce a’a, duk tatsuniya ce lamarin. Shi ya sa, har yanzu babu wani tabbaci kan hakikanin wadannan halittu ko abubuwa da aka ce suna yawo a sararin samaniya masu kama da wasu halittun da dan Adam bai san su ba. Wadanda ke tallatawa tare da yada samuwar wadannan halittu da kuma nuna cewa dole akwai su, ana musu lakabi da: “Conspiracy Theorists,” wato mutanen da ke ganin yiwuwar faruwar kowane irin abu; da wanda hankali da ala’ada zai iya dauka, da wanda ba zai iya dauka ba.

Don haka, a duk duniya gaba daya, babu zance tsayayye kan hakikaninsu da samuwarsu, balle mu yi batu kan amfaninsu. Wannan shi ne abin da zan iya cewa. Allah sa a mu dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, ina maka fatan alheri. Na dade ina bibiyar shafinka tun shekarar 2009. Ban taba aiko maka gaisuwa ba sai wannan karo. Ka huta lafiya, a gaishe min da Sadik. Daga Ibrahim Majidadi: [email protected] 

Wa alaikumus salam, Malam Ibrahim barka ka dai. Ina godiya matuka da wannan sako naka. Allah saka da alheri, Ya kuma hada fuskokinmu da alheri a duk inda muke. Na gode. Na gode. Na gode.