✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyi a kan tsaron mutuncin Uwargida (3)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku game da tsaron mutuncin uwargida a gidan…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku game da tsaron mutuncin uwargida a gidan mijinta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.

•    Tsare Mutuncin Kai A Kafofin Sadarwa: Dole ne ki tsare mutuncin kanki da na maigidanki da kuma na iyayenki a yayin da kike amfani da wadannan kafofi kamar yadda za ki tsare a fili, don haka duk wata hira, ko wani sakin fuska, ko  shige-shige da wani kawance da kika san aikata hakan a fili zai zubar da mutunci mijinki ko na iyayenki, to a wadannan kafofi ma ya zama dole ki kiyaye kada ki aikata su. Ga hanyoyin da za ki bi don tsaron mutuncinki a kafofin sadarwar zamani:
•    Tantance Abokan Hulda: Dole sai kin yi matukar taka tsan-tsan da lura sosai ga mutanen da za ki yi hulda da su a wannan kafa: Mata kadai ya halatta ki rika amsa ko aika ma sakon amintaka, kuma su ma matan wadanda kika sani kadai, domin akwai da yawa mazan da ke amfani da sunan mata kawai don yaudara.
•    Duk namijin da za ki yi hulda da shi, to ki tabbata dan uwanki ne ko kuma wani da kika sani da dadewa, sannan za ki yi hulda da shi ne ta hanyar kara wa juna sani a kan al’amuran addini da wayar da kai kadai. Ba ruwan ki da yawan gaisawa da su ko yin hirar yaushe rabo ko yawan tambaye-tambaye. Idan suka dame ki da yawan tambaya da son hira, sai ki yi shiri ki kyale su, domin ba su da damar da lallai sai kin amsa musu.
•    Duk wani dandali ko shafin da za ki shiga, to ki tabbata wanda zai zama mai alfanu ne a gare ki, wanda zai kara miki ilmi da wayar miki da kai ta fannin addini da zamantakewa ne; duk wani dandalin bayan kin shiga, kika lura ana abubuwan da ba su dace da addini ba, ko ana sharholiya da sabon Allah, to ki yi maza ki fita daga cikinsa.
•    Duk namijin da ya aiko miki da wani sakon wasika, to kada ki amsa masa ko da kuwa da amsa sallama ne, domin duk namiji mai mutunci ba zai je yana yin magana da matan da ba muharramansa ba a wadannan kafafe. Don haka sai ki yi hanzarin kange duk wani namijin da ya aiko miki sakon wasika ko ya dame ki da yawan gaisuwa; wannan ba alheri yake nufin ki da shi ba, masinjan shaidan ne da ya aiko don ya ja ki ga sabon Allah.
•    Haramun ne sanya hotunanki ko da kin sa hijabi da nikabi kin rufe fuskarki, domin na farko wannan ba wani alfanun da zai kawo miki ke da kika sanya hotunan ko wadanda suka kalli hotunan naki. Hasali ma yana iya zama sanadiyyar  jefa ki cikin wata matsala.
•    Ki yi taka tsan-tsan wajen sanya hoton yara kanana, naki ko na kawaye ko na ’yan uwa, duk da cewa hakan ba haramun ba ne, amma ya kamata a kiyaye, domin ya tabbata kambun baka gaskiya ne; idan kika sanya hoton ’ya’yanki, wani mai kambun baka ya gani ya yi sha’awa, ko da kyakkyawan nufi ya yi sha’awar, kambun bakan yana iya yin tasiri ga ’ya’yanki; ballantana kuma in mai kambun baka ya yi musu kallon hassada, kin ga in har hakan ya yi tasiri gare su ya zama garin neman kiba an samo rama ke nan.
•    Ki yi matukar taka tsan-tsan, kada ki rika tallata ni’imomin da Allah Ya yi miki a wadannan kafofi: kamar ki rika labarin zaman jin dadin da kuke yi da maigidanki; ko ki rika bagu da wata baiwa ko wani arziki da Allah Ya yi miki; ko ki rika bayyana abubuwan burgewar da ’ya’yanki suka yi. Za ki yi hakan ne don guje wa sharrin zuciya da tunanin wasu mutane, domin idan kika rubuta kika watsa ba ki san iyakar inda wannan rubutu zai je ba, kuma ba kowane mutum ne yake da tsarkakkiyar zuciya marar hassada ba. Hassadar wasu mutanen ga abubuwan alherin da kika tallata na iya janyo miki hasarar wadannan abubuwa ba tare da kin sani ba.
•    Tsare Mutunci Maigida: Yana da matukar muhimmanci ki tsare mutuncin maigidanki a wadannan kafafe, duk wani namijin da ba muharraminki ba, to babu ruwanki da shi, kada ki yarda wani namiji ya rubuta wani abu ki nuna wannan abun ya burge ki (wato ki yi liking) ko da kuwa ya burge ki din; domin wannan zai bude hanyar da shi wannan namijin da ba muharraminki ba zai miki magana; wani ma sai ya ga don ya kula ki shi ya sa kika aikata hakan.
•    Daga karshe ina ba ki shawarar ki sanar da maigidanki makullinki na shiga wadannan kafofin, kuma ki karfafa masa gwiwar ya rika budewa a-kai-a-kai yana ganin irin yadda kike amfani da su, inda ya ga kin yi kuskure, ko ya ga wani abu da bai dace ba, sai ya tunatar da ke. Wannan zai zama wani samfurin tsaro ne gare ki na ba za ki rika wuce iyaka ba, komin yadda dadin amfani da wadannan kafafe ya debe ki, domin kin san akwai yiwuwar wata rana maigidanki zai bude ya gani. Hakan kuma zai tabbatar wa maigidanki zama tsayayye gare ki ta kowace fuska da kowane bangare na rayuwarki.