✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tallafin Mai: Za a biya dillalan mai bashin da suke bi

A ranar Talatar da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin cewa a wannan makon ne za ta biya dillalan man fetur wani…

A ranar Talatar da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin cewa a wannan makon ne za ta biya dillalan man fetur wani kaso daga cikin bashin Naira biliyan 413 da suke bin ta.
karamin Ministan Man Fetur Dokta Ibe Kachikwu ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Legas, inda ya ce Majalisar Dokoki ta amince da biyan wani abu daga cikin bashin da dillalan man fetur suke bi.
Daga nan ya ce akwai jiragen ruwa guda 26 wadanda suke dauke da mai kuma kasar nan take jiran isowarsu a wannan watan. Idan suka iso hakan zai taimaka wajen wadatarsa a fadin kasar nan.
Har ila yau, ya tabbatar da cewa masu son cin kazamiyar riba ne suke kara haddasa tabarbarewar matsalar karancin mai.
Hakazalika, a wata sanarwa da kakakin kamfanin NNPC, Ohi Alegbe ya fitar a makon jiya, ya nemi afuwar ‘yan Najeriya saboda wahalar da suke sha kafin samun man fetur, yana mai cewa ana daukar kwararan matakai domin shawo kan matsalar.
Kimanin wata guda ke nan ake fuskantar matsalar karancin man fetur a fadin kasar nan, kuma kamar wasa matsalar sai kara kamari take yi.