✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta haramta aske gemu da jin kida a Afghanistan

An haramta wa shagunan aski da gidajen wanka jin kida ko aske gemu.

Gwamnatin Taliban a kasar Afghanistan ta haramta aske gemu ko jin kida a shagunan aski a fadin kasar.

Sabuwa dokar tana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Hukumar Yadda Kyawawan Dabi’u da Hana Fitsara ta fitar a ranar Lahadi.

“Daga yau (Lahadi) aske gemu da jin kida sun haramta a shagunan aski da gidajen wanka.

“Duk shagon aski ko gidan wanka da aka kama yana aske wa maza gemu ko sanya kida, za a yi masa hunkuncin da Shari’ar Musulunci ya tanadar”, inji sanarwar.

Ta kara da cewa wajibi ne duk shuganan aski su bi tsarin Musulunci game da aski da kuma cika gemu, “Kuma babu mai damar yin korafi,” saboda Musulunci ya hana aske gemu.

Masu shagunan aski da gidajen wanka a Kabul, babban birnin kasar, sun tabbatar cewa sun samu takardar umarnin daga hukumar Hisbah ta kasar.

“’Yan Taliban na zuwa suna hana mu aske wa mutane ko rage musu tsayin gemu.

“Wani daga cikinsu ya shaida min cewa za su iya turo masu leken asiri domin su kama masu kunnen kashi,” inji wani mai shagon aski a Kabul.

Haramta jin kida da aske gemu na daga cikin sabbin dokokin da gwamnatin Taliban ta dawo da su a Afghanistan, kasa da wata guda da ta fara gudanar da mulki a kasar.

Idan ba manta ba, tun da farko gwamnatin ta haramta cakuduwar mata da maza a jami’o’i, tare da wajabta wa mata sanya dogayen hijabai.

A makon jiya ne gwamnatin ta sanar cewa za ta dawo da zartar da hukuncin haddi a kan duk wanda aka samu da laifin da ya cancanci  hakan.

A ranar Asabar, an zartar wa wasu mutum hudu da ake zargi da garkuwa da mutane hukuncin kisa, tare da rataye gawarwakinsu a yankin Herat.

Gwamnatin ta ce ta yi hakan ne domin ya zama jan kunne ga masu yunkurin aikata irin laifin.

Tun a lokacin da Taliban ta kwace mulki a ranar 15 ga Agusta, 2021, ta sanar cewa za ta zartar da shari’ar Musulunci 100 bisa 100, duk da cewa ta ce ba za ta tsananta ba.

Kasashen duniya dai na yi wa Taliban kallon mai tsattsauran ra’ayin addinin Islama, wanda suke gani a matsayin tauye hakkin bil Adama ne.