✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talakawa na iya taimakawa wajen samar da canjin gwamnati – Dokta Lame

Dokta Ibrahim Yakubu Lame, tsohon Ministan Harkokin ’Yan sanda, kuma jigo a Jam’iyyar APC da ke neman tsayawa takarar Gwamnan JIhar Bauchi ya kira taron…

Dokta Ibrahim Yakubu Lame, tsohon Ministan Harkokin ’Yan sanda, kuma jigo a Jam’iyyar APC da ke neman tsayawa takarar Gwamnan JIhar Bauchi ya kira taron manema labarai inda ya yi tsokaci kan matsalolin Arewa da siyasar Najeriya:

Aminiya: Me za ka ce game da yadda zabubbukan Jam’iyyyar APC suka gudana a Jihar Bauchi da kasa?
Dokta Lame:  Na yi farin ciki sosai kan yadda lamura suka gudana, dubban mutane a Bauchi suka fito suka zabi abin da suke so aka kuma ba su, wannan kalubale ne gare su na su zauna su tabbatar sun gina jam’iyyarsu ta APC bisa ka’idar dimokuradiyya su sa jam’iyya a gaba ba bukatar wani ba. Su sani an fid da kwararrun shugabanni saboda mu samu damar gina jam’iyya yadda za a samu gwamnati mai adalci da za ta bunkasa arzikin kasa da ba jama’a abin da zai amfane su. Da fatar za mu samu zarafin fitar da shugabanni kwararru ta hanyar nuna wa duniya halin kwarai da muke da shi kuma mu nuna shugabanni a yanzu ba za su fito ta hanyar masu mayar da jam’iyya kamar kamfani ba, wato ’yan jari-hujja masu cutar da mutane. Mu fitar da shugabanni daga kasa har sama wadanda suke da kyau don kada mu koma gidan jiya.
Aminiya: Ina aka tsaya game da batun neman takararka ta Gwamnan Jihar Bauchi a Jam’iyyar APC?
Dokta Lame: Na jima ina fadi cewa ba zan fito takara ba, sai an kafa shugabannin jam’iyya, an gama na jiha da na kasa, kuma nan ba da jimawa ba zan kammala shawarata ta fitowa neman takarar Gwamnan Jihar Bauchi insha Allahu.
Aminiya: Ana zargin jam’iyyarku ta APC da taimaka wa ’yan ta’adda da suke kai hari suna kashe mutane da kone dukiyarsu a Arewa me za ka ce?
Dokta Lame:  Zargi ne na wanda ya kasa tabuka komai kuma yake neman kai kasar cikin hallaka, don haka ina gani wannan rashin sanin ya kamata ne da kuma rashin iya aiki ko rashin son a yi aiki. Amfanin gwamnati shi ne bayar da tsaro ga jama’a da dukiyarsu da rayukansu da addininsu da mutuncinsu da walwalarsu. Duk gwamnatin da ta kasa ya nuna ta ki yi ne ko kuma ta gaza. Su ce ’yan adawa na kawo musu cikas karya ne. Idan da a wata kasa da aka san ’yanci ne da tuni an kore su daga kan mulki tunda sun gaza dole su sauka.  Wannan magana ce mai muni da ’yan Najeriya ya kamata su fahimci cewa wadannan mutane ba za su iya ba, don haka mafita ita ce kada mu sake zabar su, shi ne amfanin dimokuradiyya, don a ba mutum ya yi idan ya gaza wasu su zo su kama don a samu gyara.
Aminiya: Kana cikin kungiyar Dattawan Arewa, amma kullum kashewa da kona rayuka da dukiyar ’yan Arewa ake yi, mene ne shawararka ga ’yan arewa da Gwamnatin Tarayya?
Dokta Lame: Mun ba Gwamnatin Tarayya shawara a rubuce, ina cikin wadanda suka je gaban Shugaban kasa kan batun kuma mun bayar a rubuce mun fada a jaridu amma sun ki, don haka a takaice dole a duba batun jami’an tsaron da suke aiki a ko’ina domin akwai zargi mai yawa. Ya kamata a ba su kayan aiki da lura da yanayin aikinsu. Kuma dole a ji damuwar mutanen da wannan abu ke faruwa a wurarensu a karbi shawararsu. Kuma dole a bayar da kayan tallafi ga mutanen wajen saboda mutanen ba sa iya zama a gidajensu ba sa iya noma ba sa iya kasuwanci. Don haka abu ne da ya kamata a yi gaskiya, kamar abin da marigayi ’Yar’aduwa ya yi a can koda bai yi kamar nasa ba dole a kamanta. Saboda an san masu taimaka wa wannan harka mun bayar a rubuce mun fada wa duniya dole ne mu shugabannin Arewa mu ci gaba da tursasa wa wadannan mutane su kawo karshen wannan matsala. Kuma gwamnatocinmu na jihohi dole su tashi tsaye su hada kai wajen ganin an kawo karshen wannan lamari. A tashi tsaye a kafa gwamnatoci na gaskiya da za su kawo ci gaba da yin aikin da ya dace ga mutane da samar da aikin yi da kau da barna don a rage shigar da mutane cikin ta’addanci.
Aminiya: Wasu na ganin an kulla wani yaki ne da Arewa da gangan, kullum ana kashe mutane ana ganin kun yi shiru, me za ka ce don jama’a su yarda da ku?
Dokta Lame: Dole ne mu samar da canji game da yadda ake yi mana jagoranci, ba mu da wata hanyar da ta wuce wannan, iyaka idan kun ga an cutar da ku bayan shekara hudu ku taru ku juya gwamnatin da kuri’unku. Shi ya sa muke ta kokarin gina akidar canji ta yadda ake tafiyar da gwamnati ta hanyar barin barna da tauye hakkin mutane shi zai kawo zaman lafiya da son juna da arzikin kasa. Ba mu zauna a gidan gwamnati muna kwasar dukliyar jama’a muna gina gidajen da ba za mu kwana ciki ba, ko sayen motocin da ba za mu iya shiga ba. Gwamnati adalci ne ba alfarma ba, don haka ina tabbatar da cewa za mu iya sauya salon mulki da gyara rayuwar jama’ar Jihar Bauchi da Najeriya matukar aka ba mu goyon baya da hadin kai da shawarwarin da suka dace. Muna fata Allah Ya taimake mu Ya sa talakawa su fahimci abin da ya dace su yi don sama wa kansu mafita daga cikin wannan kangi da muka shiga.