✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Take-taken gwamnatin Buhari so take ta kashe jami’o’in gwamnati – ASUU

Kungiyar ta yi zargin gwamnati na son kashe jami’o’i kamar yadda ta kashe firamare da sakandiren gwamnati

Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) reshen Jami’ar Legas, Dokta Dele Ashiru, ya yi zargin cewa take-taken gwamnatin Muhammadu Buhari ya nuna tana kokarin kashe jami’o’in gwamnati ne a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust ta shirya a shafin Twitter ranar Juma’a.

A ranar Litinin ce kungiyar ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da wata uku, lamarin da ya jawo cece-kuce, tare da shirya zanga-zangar dalibai a sassa daban-daban na Najeriya.

Dokta Dele Ashiru ya ce wannan shi ne karo na uku da ake rufe jami’o’i a Najeriya tun lokacin da Shugaba Buhari ya dare karagar mulki.

Ya ce, “Tun da suka hau mulki ake ta faman rufe makarantu. Wannan shi ne karo na uku. Babban abin takaicin shi ne yayin da makarantun ke rufe, sun ci gaba da gangamin siyasarsu, ko a jikinsu.

“Amma mu a matsayinmu na kungiyar da ta san ya kamata, mun fuskanci inda suka dosa. So suke yi su karasa lalata jami’o’in gwamnati.

“Kamar yadda suka lalata firamare da sakandiren gwamnati, ta yadda makarantunsu na kudi za su sami isassun dalibai.

“Abin da zai ba ka mamaki, yayin da ake tsaka da yajin aikin, mutane na kiran a sake bude makarantun, sai ga shi gwamnati na ta ba jami’o’i masu zaman kansu lasisi.

“’Ya’yan talakawa nawa ne za su iya biyan wadannan kudaden? Abin da muke so ’yan Najeriya su fahimta shi ne saboda su muke wannan fafutukar don mu ga gwamnati ta inganta su. In ba a yi abin da ya kamata ba, nan da wani lokaci za a neme su a rasa,” inji Shugaban na ASUU.