Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta ce kimanin takardun fasfo da sauran takardun tafiye-tafiye dubu dari da hamsin sun bace ko kuma an sace su.
Kakakin hukumar, Sunday James ya shaida wa kamfanin dillancin labarai an Najeriy (NAN) cewa sakamakon haka teburin hukumar na NIS INTERPOL i-24/7 ya sanya bayanan takardun da aka sace ko suka bace (STLD) a kundin bayanan hukuma ‘yan sanda na ta Duniya (IPSG).
- Atiku ya yi wa Buhari shagube kan karin farashin fetur
-
Ya ce INTERPOL i-24/7 babbar dandamali ne da hedikwatar NIS ke kula da shi kuma shugaban hukumar, Muhammad Babandede na da cikakken bayani game da halin da ake ciki da kuma matakan ka daka dauka.
“Nasarar tattarawa da sanya wannan adadi na takardun STLD a tsakanin kasashe a kundin bayanan IPSG gagarumar nasara ce”, inji James.
“Wannan kokarin ne na jami’an hukumar na dakile yunkurin satar bayanan jama’a da aka san ‘yan danfara masu aikata manyan laifuka a fadin duniya da yi ta hanyar amfani da SLTD.
“Shigarmu IPSG shi ne na farko a Afirka kuma na 54 a duniya.
“Yanzu Najeriya ta sanya bayanan SLTD guda 150,000 a cikin APSG-Lyon da ke kasar Farasan ta amintacciyar hanya a ranar Litinin 7 ga Satumab, 2020.
“An samu wannan gagarumar nasara ce da tallafin IPSG da Ofishin Cibiyar tara bayanai ta Amurka (USNCB) da ke Abuja da kuma NIS”, kamar yadda ya bayyana.