✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima

Ganduje ya yi jawabi ba tare da ambaton sunan Shettima ba, wanda hakan ya haifar da rikici.

An samu saɓani a wani taron shugabannin jam’iyyar APC a yankin Arewa Maso Gabas da aka gudanar a Jihar Gombe.

Rikicin ya fara ne bayan da Kwamared Mustapha Salihu, Mataimakin Shugaban APC na ƙasa mai kula da Arewa Maso Gabas, ya bayyana goyon bayansa ga takarar Shugaba Bola Tinubu don ya sake tsayawa takara a karo na biyu.

Sai dai bai ambaci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ba.

Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga yankin sun halarci taron, ciki har da gwamnoni, ministoci, da ‘yan majalisa.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, shi ma ya halarci taron.

Bayan Salihu ya gama jawabi, wasu daga cikin mahalarta taron sun fusata.

Take suka fara yi masa ihu, wasu ma suna barazanar kai masa hari.

Sai jami’an tsaro sun fito da shi daga ɗakin taron don kare lafiyarsa.

Don kwantar da rikicin da ya taso, Mataimakin Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Bukar Dalori, ya fito ya bayyana goyon baya ga Tinubu da kuma Shettima don su ci gaba da mulki.

Amma lamarin ya ƙara dagulewa bayan da Ganduje ya yi jawabi, inda ya ayyana goyon bayansa ga Tinubu kaɗai, ba tare da ya ambaci Shettima ba.

A yayin jawabin da ya yi na kusan minti 10, bai ambaci sunan Shettima ba.

Shi ma sai da jami’an tsaro suka fita da shi daga wajen taron saboda gudun rikicin da zai je ya dawo.

Shettima dai ɗan Jihar Borno ne, ɗaya daga cikin jihohin yankin Arewa Maso Gabas.

Mutane da dama sun ji ba ɗadi kan rashin ambaton sunan a wajen taro da aka yi a yankinsa.

Taron ya kare cikin gaggawa saboda tashin hankali.