Mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed, ya ce takarar Musulmi da Musulmi ba komai ba ce face yaudara.
Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci game da mika takarar shugabancin majalisar dattawa da APC ta yi, a lokacin hirarsa da gidan Talabijin na Channels a ranar Talata.
Ya ce kamata ya yi a bari ’yan majalisar su zabi wanda suke so ya jagorance su.
A cewarsa, ya kamata a bari yankin Arewa Maso Yamma ya samar da Shugaban Majalisar Dattawa, saboda kuri’unsu ne suka bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu nasarar lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Da yake tsokaci game da takarar Musulmi a Jihar Kaduna, ya ce “Me shi (El-Rufai) ya yi wa Musulmi? Ya rushe gidajensu. Kashi 95 na gidajen da gine-ginen da ya rushe na Musulmi ne. Don haka yaudara ce kawai.
“’Yan siyasa sun gurbata abubuwa da dama. Sun mayar da komai ya koma siyasa.
“Da farko mun idanunmu a bude suke. Suna lalata tsarin siyasa ta hanyar kawo addini a cikinsa.
“Idanunmu sun bude yanzu. Suna yaudarar mutane da cewar suna wakiltarsu ne,” in ji shi.