Wani Babban Lauya a Najeriya Babatunde Ogala ya ce zabo Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takara da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya yi bai saba wa wata dokar kasa ba.
Lauyan wanda shi ne Shugaban Sashen Shari’a na Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambaya ta cikin shirin wani gidan Talabijin mai zaman kansa a Najeriya, kan ce-ce-ku-ce da wasu ke yi game da zabo Musulmi a matsayin abokin takarar shugaban kasa da APC ta yi.
- ’Yan bindiga sun kashe, sun sace ’yan yawon Sallah a Katsina
- DAGA LARABA: Yadda Matsalar Tsaro Da Rashin Tsari Suka Ruguza Ilimi a Zamfara
Ya ce zabo shi kansa Tinubun a matsayin dan takarar shugaban kasa da jam’iyar ta yi abu ne da ya dace al’umma su yi alfahari da shi, musamman ma ’yan kudancin kasar da kungiyar gwamnoninsu ta dage sai wanda ya fito daga yankin nasu ne zai y takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Ya ce: “Ka duba me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce, sashi na 14 da 15 sun yi bayani kan wannan turka-turka, inda suka bayyana dole ne a zabo ’yan takarka da abokansu ta hanya mai tsafta da adalci, amma bai ce komai ba kan addini”.
Haka kuma a cewarsa “dokar ta yi magana kan wakilci daga mabambantan al’umma, ka ga har wa yau dai ba ta ambato addini ba, ka ga batun nuna bambanci ga wan addini duk zancen son rai ne kawai”.
Ya ce zabo abokin takara daga karamar kabila da Tinubun ya yi abu ne mai kyau da ya kamata a yaba masa, domin abu ne da ya sabawa wanda jam’iyar adawa ta PDP ta yi, na zabo dan Arewa a matsayin dan takararta na shugaban kasa.
“Idan kuma ana nufin ta fuskar manyan kabilu uku da muke da su ne, wato Hausa da Ibo da Yarabawa, to Kashim Shettima Kanuri ne da ya fito daga Jihar Borno, wacce karamar kabila ce a Arewacin Najeriya, saboda haka ka ga dai ba a saba wa waccan dokar ba ke nan”, in ji shi.
Sai dai ya ce yaznu dai jam’iyarsu ta APC ta maida hankali kan yadda za ta samu nasara a zabe mai zuwa, inda ya nanata cewa “ba wai suna gina shugabannin addini ba, suna gina shugabannin da za su jagoranci kasar nan ne ba tare da wata matsala ba.
Lauya Ogala ya ce yana da yakinin Kashim Shettima zai taimaka wa APC lashe zaben 2023.