Shehu dan Fodiyo ya zaba wa Yakubu wurin zama:
Da Shehu ya ji haka sai ya ce da Yakubu: “Ka zauna nan yamma kusa da inda kake, wato yamma da Inkil. Wannan wuri yana da kyau sai dai fatara da talauci kawai. Amma fa addininka da zuriyarka babu abin da zai matsa su har a gama da Mahdi.” Yakubu ya ce da Shehu ya yarda, sai dai wurin akwai macizai, domin yana tsakanin duwatsu ne. Shehu ya ce: “In dai macizai ne zan taimake ka da bidar tsarinsu daga Allah. Zan taimake ka da rokon Allah kan al’amarin garinka duka.” Shehu ya ce: “Batun macizai in dai a cikin garinka ne, maciji ba zai ciji kowa ba. Kuma da zai yi cizon ba za a mutu ba, sai fa idan aljani ne. Kuma ina shaida maka cewa duk bakon da ya zo garinka ya kwana bakwai ko da zai koma garinsu, sai ya shekara zuciyarsa na garinka. Wanda ya shekara a garinka, sai ya zama naka. Kuma mutumin cikin garinka dan shekara bakwai sai ka ga suna turereniya da dan shekara 80 wajen shiga masallacin Juma’a. Mutumin kasarka (garinka) idan ya hau dutse ya noma hatsi, (sai) ya yi kyau kamar na jigawa. Amma fa mutumin garinka in dai ba bako ba ne, ba zai yi dukiya mai yawa ba, sai dai ya samu abinci (rufin asiri). Domin idan ya yi dukiya mai yawa, yadda kasarka ke da tauri haka zuciyarsa za ta zama.”
Ya kara da cewa: “Kuma idan ka je gina ganuwar garinka, ka sanya goshin dutsen Warinje ya zamo daga cikin garinka. Idan ka yi yadda na ce, insha Allahu babu abin da zai tayar da garinka, kuma babu dattijon da zai zo ya ci garinka.”
Yakubu ya gina ganuwar Bauchi:
Sai Yakubu ya taso daga Sakkwato ya komo gida. Bayan ya huta sai ya taso daga Inkil ya zo inda zai kafa garinsa, yana cikin zagayawa ne ya hango wani mutum zai shige, ya nufi Dutsen Idi. Sai Yakubu ya kira shi. Da mutumin ya iso suka gaisa, Yakubu ya ce, masa: “Kai bako ne ko a nan kake?” Sai mutumin ya ce: “Nan nake ga gidana can a kan dutse (wato dutsen da ke kusa da masallacin Idi na Bauchi). Sai Yakubu ya tambayi mutumin sunansa, ya ce shi maharbi ne kuma sunansa Baushe, amma yara suna kiransa Baushi, har ya zama yanzu manya da yaran suna kiransa da Baushi. Sai kuma ya tambayi Yakubu sunansa da inda ya fito. Yakubu ya fada masa. Sai Baushi ya ce: “Ko kai ne malamin nan da ake fadi yana Inkil?” Yakubu ya ce, eh. Sai maharbin nan ya ce: “Na gode Allah da Ya nufe ni da ganinka. Allah Ya ba ni albarkacinka.” Yakubu ya ce masa, shi ma ya fito ne yana yawon duba inda zai kafa garinsa. Kuma idan Allah Ya yarda ya kafa garin zai sanya masa sunansa wato Baushi. Sai maharbin ya ce da Yakubu, zai jira shi ne ya je gidansa ya komo ko zai koma gida shi ya je ya iske shi. Sai Yakubu ya ce masa duk wanda ya zaba daya ne. Sai maharbin ya ce da Yakubu ya koma gida gobe zai zo ya ga yadda ya iske gidan.
Washegari da sassafe sai ga maharbin dauke da damin hatsi, matarsa dauke da kwando cike da gari, sai dansa kuma dauke da kaji, suka je gidan aka yi musu iso suka shiga suka gaisa da Yakubu. Ya ce da Yakubu ga wadannan kaya su ne godiyarsa gare shi, kuma yana murna da jin cewa zai sanya wa garin nan nasa sunansa. Wannan shi ne dalilin sabawar Baushi da Yakubu.
Ana nan Yakubu ya kafa garin ya sanya masa sunan Baushi kamar yadda ya yi alkawari. Kuma daga nan ne garin Bauchi ya samo wannan suna nasa.
Lokacin da aka gina ganuwar Bauchi, garin ya zaunu kuma aka samu nasara, Malam Yakubu ya tara jama’arsa ya yi musu godiya ya ce, to yanzu kuma sai a yi sarautu. Ya ce: “Ina son in nada sarakunan jihadi. Kai Hasan yau kai ne Madakina, ni kuma yau ni ne sarkinka. Faruku kuma kai ne Galadimana. Kai kuma Muhammadu Kusu kai ne Sarkin Yakina.” Da aka tabbatar da wadannan sai kuma Abdu ya ce: “Yau kuma ni ne Wambautarka.” Nan take sai Yakubu ya ce masa: “ Yau (Abdu) kai ne Wambaina.”