✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaitaccen tarihin ginin Taj Mahal

Taj Mahal daya na daya daga cikin abubuwan al’ajabi bakwai da ake da su yanzu haka a duniya. Wannan gini na Taj Mahal tarihi ya…

Taj Mahal daya na daya daga cikin abubuwan al’ajabi bakwai da ake da su yanzu haka a duniya. Wannan gini na Taj Mahal tarihi ya bayyana cewa wani kabari ne da Sarki Shah Jahan ya sa aka gina wa matarsa ta uku mai suna Mumtaz Mahal domin tunawa da ita a matsayinta na wacce ya fi so da kauna a rayuwarsa. Wannan kasaitaccen gini na Taj Mahal yana yankin Agra ne na kasar Indiya, kuma an bayyana cewa shi ne kyautar soyayya mafi tsada a duniya. Ginin yana da tsawon mita 73 (daidai da kafa 240) Ustaz Ahmad Lahauri shi ne ya zana taswirar ginin.
Sarauniya Mumtaz Mahal ta rasa ranta ne lokacin da ta zo haihuwa ta 14. Mutuwarta ta girgiza Sarki Shah Jahan matukar girgizawa inda ya sha alwashin yi mata kyautar da za a rika tunawa da ita har duniya ta tashi.
Haka kuwa aka yi Sarki Shah Jahan ya tura sassa daban-daban na duniya aka nemo masa kwararrrun magina sama da dubu 20 suka kama aiki dare da rana domin wannan gini na Taj Mahal. An fara ginin ne a shekarar 1632 aka kammala a shekarar 1653, kimanin shekara 22 aka shafe ke nan ana aikin ginin. A wancan lokacin ginin ya ci kimanin Rufin Indiya har milyan 32, wanda darajarsu a yanzu sun kai Rufi biliyan 52.8, (daidai da Dalar Amurka miliyan 827).
Bayan an kammala ginin a shekarar 1653, sai Sarki Shah Jahan ya sa aka tara kwararrun maginan da suka yi aikin tare da ba da umurnin datse hannayensu. Dalilansa na wannan danyen aiki, shi ne don kada su je su sake gina wani makamancinsa a wani wuri.
A yau an wayi gari ginin Taj Mahal mai shekara 383, shi ne gini guda daya da babu makamancinsa a duk fadin duniya wajen tsari da daukar hankali. A halin yanzu gawar Shah Jahan da na matarsa Mumtaz Mahal na rufe su ne a cikin wannan katafaren ginin da ya zamo tamkar sansanin ’yan yawon bude-ido daga sassa daban-daban na duniya (an ce kimanin mutum miliyan uku suka ziyarci ginin a shekarar 2003).
Babban jagoran ginin wanda shi ma aka datse hannayensa, suruki ne ga Sarki Shah Jahan. Tarihi ya bayyana cewa ko tafin hannun mutum kawai ya gani ba tare da ganin fuskarsa ba zai iya zuwa ya zana mai hannun a kan dutse daidai ba tare da kuskure ba.
Sani Ahmad Giwa (Marubuci kuma dan jarida da ke Kaduna)