Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PRP a zaben shekara ta 2019, Salihu Sagir Takai ya fice daga jam’iyyar ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.
Mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Abdulahi Musa Huguma wanda ya tabbatar da sauya shekar ya ce tsohon dan takarar ya yanke shawarar ne bayan tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki a siyasarsa.
Da ma dai Takai a jam’iyyar PDP yayi takara a zaben 2015 kafin daga bisani ya fice koma PRP bayan da alamu suka nuna ba zai sami takarar gwamna a PDP ba.
Huguma ya ce, “Malam Salihu ya koma jam’iyyar APC ne a matsayin mamba kuma ya shiga ne tare da dukkan masoya da magoya bayansa daga kananan hukumomi 44 dake jihar Kano, kuma bay a koma bane don ya tsaya kowacce irin takara.
“Zai kasance mai bin dukkan dokokin jam’iyyar sau da kafa tare da kuma yin biyayya ga shugabancin jam’iyyar a jihar. Kamar yadda kowa ya sani, Malam mutum ne da yake girmama ra’ayin magoya bayansa, kuma hakan ce ma ta say a yanke wannan shawarar”, in ji Huguma.
Tsohon shugaban karamar hukuma kuma tsohon kwamishina a ma’aikatun ruwa da ta kananan hukumomi, a na ganin Takai a matsayin na hannun daman tsohon gwamnan jihar kuma sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Ibrahim Shekarau.
Tauraruwarsa ta fara haskawa ne a siyasance lokacin da Shekarau ya tsayar da shi a matsayin dan takarar gwamnan jihar a zaben shekarar 2011 a karkashin jam’aiyyar ANPP, ko da yake a zaben 2019 sun raba gari a siyasance.
A shekarar 2015 ma ya sake tsayawa takarar gwamnan a karkashin tutar jam’iyyar PDP, ko da yake a lokacinma bai kai ga nasara ba.
Takai dai bai fadi ainihin makasudin komawarsa APC ba, amma ya ce ya ya yanke shawarar ne bayan tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki a siyasarsa.