✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddamar zaben Gwamnan Anambra

Bisa furucin shugabanta Farfesa Attahiru Jega, Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ba ta yi aikinta yadda ya kamata ba, wajen gudanar da zaben Gwamnan Jihar…

Bisa furucin shugabanta Farfesa Attahiru Jega, Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ba ta yi aikinta yadda ya kamata ba, wajen gudanar da zaben Gwamnan Jihar Anambra na ranar 16 ga Nuwamban bana ba.
Kuma lura da abin da ya biyo bayan zaben ya nuna an tafka ba daidai ba. Bayyan cewa zaben bai kammala ba, kamar yadda INEC ta yi, ya ba jami’anta damar su auna kuskuren da aka yi; sai dai bayanin Jega na cewa babu wata kwakkwarar shaida da za ta sa a soke zaben, kamar yadda wasu jam’iyyu uku da suka shiga zaben suka nemi hukumar zaben ta yi domin zama hukunci na karshe wani abu ne da za a warware shi a bangaren shari’a.
Sannan akwai sabani a tsakanin ’yan siyasa su ya su da kuma a tsakanin masana shari’a game da gudanar da zaben cike gibi da INEC ta shirya yi a gobe Asabar 30 ga Nuwamba, kan ko yana da madogara a doka.
Kwana biyu bayan gudanar da zaben, Babban Jami’in Tattara Sakamakon Zabe na INEC kuma Shugaban Jami’ar Kalaba, Farfesa James Epok ya bayyana cewa babu dan takarar da ya samu kashi 25 a biyu bisa uku da ake bukata a kananan hukumomin Jihar Anambra 21 domin a bayyana ya lashe zaben. Wani abin da ya kara rikirkita lamarin shi ne yawan kuri’un da aka soke, kimanin dubu 413 da 113. Kimanin mutum miliyan daya da dubu 763 da 751 ne INEC ta yi musu rajista domin gudanar da zabe; kuma mutum dubu 451 da 826 kacal ne aka tantance don yin zaben. Kuma halattattun kuri’un da aka kada su ne dubu 413, 005, yayin da haramtattu suka kasance dubu 16 da 544, gaba daya an kada kuri’a 429 da 549. Daga cikin kuri’un da aka soke mafi awa sun fito ne daga karamar Hukumar Idemili a Arewa mai kuri’u dubu 89 da 997.
Sakamakon zaben ya nuna Jam’iyyar APGA mai mulkin jihar da ta tsayar da Mista Willie Obiano a matsayin dan takararta ta samu mafi yawan kuri’un da aka kada, wato kuri’a dubu 174 da 710, yayin da Mista Tony Nwoye na Jam’iyyar PDP ya zo na biyu da kuri’a dubu 94 da 956. dan takarar Jam’iyyar APC, Dokta Chris Ngige ya samu kuri’a dubu 92 da 300, yayin da dan takarar Jam’iyyar LP, Mista Ifeanyi Uba ya samu kuri’a dubu 37 da 466. Gaba daya ’yan takara 25 ne suka fafata a zaben.
Babban kalubalen da ke fuskantar INEC shi ne warware matsalar halin da jami’in zabenta mai kula da Idemili ta Arewa ya nuna, inda dimbin kuri’un da aka soke suka fito, wadanda za su iya yin gagarumin tasiri kan sakamakon zaben na 16 ga Nuwamba.
An ruwaito Farfesa Jega daga baya yana cewa: “Jami’in Zabe mai kula da Idemili ta Arewa saboda wani dalili mai daure kai ya rikirkita rabon kayayyakin zabe.”
Ya ce jami’in ya rike wasu takardun sakamakon zaben ya raba wasu ‘takardun sakamako na bogi.’
“Muna da karfin imanin cewa akwai wani hadin baki tsakanin jami’in zaben da wasu da ba a gano ba domin lalatta zaben,” inji Shugaban na INEC.
Duk da cewa Farfesa Jega ya ce an mika wancan jami’in zabe da ake magana kansa da wani sufabaiza da ke kula da yankin ga ’yan sanda, yana da matukar muhimmancin ga zaben Gwamnan Jihar Anambra don yinsa cikin gaskiya har a kammala shi, ya zama wajibi a fallasa wadancan ‘da ba a gano ba,’ kuma a hukunta su yadda ya kamata. Zabe a Jihar Anambra kusan koyaushe yana da matsaloli. Tun dawowar mulkin farar hula a kasar nan a 1999, zaben Gwamna a jihar cike yake da nau’o’in rashin bin ka’ida ciki har da tilsta dan takara dab da zabe da da sacewa da cika akwatunan zabe da kuri’un karya.
Yanzu ne hukumar zaben ya wajaba ta sanya aya ga haka, kuma ta tabbatar wadannan keta dokoki ba su sake aukuwa ba, akalla kada su auku irin yadda ake gani a jihar a shekarun nan.
Domin cimma nasarar haka, wajibi ne INEC ta yi wankan sarki ga daukacin jami’anta da rawar da ake zargin sun taka ta hada baki da jami’an gwamnatin Anambra don lalata zaben na 16 ga Nuwamba.
Abin da ya faru ya nuna har yanzu akwai jan aiki a gaban INEC, kuma ya sanya alamar tambaya kan irin shirinta na gudanar da inganaccen zaben kasa a shekarar 2015. Jam’iyyun PDP da APC da LP, sun bayana balo-balo za su kaurace wa zaben cike gibin. Ya rage ga INEC ta magance korafinsu. Wajibi ne hukumar ta dauki darasi daga abin da ya faru, tare da aiki da darasin da ta koya don ganin ta magance aukuwar haka a zaben gwamnoni – a jihohin Osun da Ekiti- a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaben kasa a shekarar 2015.