✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Takaddama ta barke tsakanin Pantami da Abike Dabiri

A karshen makon jiya ne shugabar Hukumar Da Ke Kula Da ‘Yan Najeriya a Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa ta zargi Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami…

A karshen makon jiya ne shugabar Hukumar Da Ke Kula Da ‘Yan Najeriya a Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa ta zargi Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami da dakatar ma’aikatan hukumarta daga shiga wani ofishin da gwamnatin tarayya ta ba su.

Rahotanni na cewa cacar-baki ta barke tsakanin Pantami da Dabiri-Erewa ne, kan wanda a cikinsu ke da hakikanin hakkin mallakar ofoshin da ke kan titin Airport Road, na gundumar Mbora a Babban Birnin Tarayya Abuja.

A watan Fabrairun da ya gabata ne dai a ruwaito jami’an tsaro da ake zargin ministan ne ya ba su umarni, suka fatattaki ma’aikatan hukumar daga ginin ofishinsu a Abuja.

Sai dai kuma ministan wanda ya yi magana ta bakin masu taimaka masa ya ce sam ba shi da masaniya a kan zargin.

Amma Dabiri-Erewa a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce Pantami ne ya umarci jami’an tsaron kada ma su bar ma’aikatan hukumarta su shiga ofishin, wanda Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Kasa (NCC) ce ta damka musu tun da farko.

Har ila yau a wani bidiyo da ta wallafa a shafin nata, Dabiri-Erewa ta kwatanta yadda wasu mutane dauke da makamai suka yi wa ofoshin tsinke suka hana ma’aikatanta shiga.

 Shi  daigini ofishin da ake takaddama a kai wanda wani sashe ne na ginin shalkwatar hukumar NCC yana gundumar Mbora ne na Babban Birnin Tarayya Abuja.

Dabiri-Erewa ta ce, “Kimanin shekara guda ke nan ba mu da ofis sai wannan da NCC ta ba mu. Amma kwatsam cikin kwana biyu sai Ministan Sadarwa Pantami ya turo a ka kore mu, kuma babu abin da ya faru.

“Mu kan taimaki juna a matsayinmu na hukumomin gwamnati, wanda hakan ne ma ya NCC ta ba mu wajen da za mu dan rabe.

“Lamarin ya faru ranar Talata lokacin ma ina kasar Itofiya. Kamar da ba’a aka kira ni ake shaida min ga abin da yake faruwa a ofishinmu.

“Ko da na dawo ranar Juma’a sai na iske jami’an tsaro jibge a wajen sun hana mu shiga. Bai kamata hakan ta faru tun da dai ni da shi duk gwamnati muke yi wa aiki,” inji ta.

Ta kara da cewa, “Na yi korafi a hukumance amma ba abin daaka yi a kai.

“Maganar da nake yanzu haka hawa guda yana nan a kulle ba komai a ciki. Hatta kwamfutoci da sauran na’urorin da muke amfani da su duk suna ciki a kulle”.

To sai dai a martininsa ta shafi da na Twitter ranar Lahadi, Minista Pantami ya bayyan zargin a matsayi ‘shirgegiyar karya’.

“Wannan wata shirgegiyar karya ce kawai ta yi! Hukumar NCC da ta mallaki ginin ta karyata zargin (da Dabiri-Erewa ta yi) a shafukanta na zumunta.

“Ministan bai taba tura wasu masu dauke da makamai don su tashe su ba. Ya kamata mu rika yi wa kanmu adalci,” inji Pantami ta shafinsa na twitter.

Rahotanni dai sun nuna cacar-baki ta barke tsakanin Pantami da Dabiri-Erewa a kan hakikanin wanda yake da hakkin mallakar ofoshin da ke kan titin Airport Road, na gundumar Mbora a Babban Birnin Tarayya Abuja.