Wasu tagwayen hare-hare da aka kai yankin Aleppo da ke Arewacin Syria, sun yi ajalin akalla mutum 14 yayin da gwammai suka jikkata.
A yayin da kawo yanzu ba a kai ga tantance wanda ya kai farmakin ba, Gwamnatin Turkiyya ta dora alhakinsa a kan mayakan Kurdawa na kungiyar YPG.
- Yadda ’yan bindiga ke cin karensu ba babbaka a Zariya
- Isra’ila: Netanyahu ya sha kaye bayan shafe shekara 12 a matsayin Fira-Minista
Sai dai tuni kungiyar Syrian Democratic Forces wadda YPG ke gudanarwa ta musanta kai harin.
Bayanai sun ce harin na farko ya afka wa bangaren gidajen fararen hula, a yayin da na biyu kuma ya fada kan wani Asibiti da ke garin Afrin.
Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna gawarwakin mutane a baraguzan ginin Asibitin Al-Shifaa da ke garin na Afrin.
Rahotanni sun ce daga cikin wadanda suka mutu akwai ma’aikatan lafiya da kuma kananan yara.
Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa, IRC, ta ce wannan shi ne hari na 11 da aka kai kan wata cibiyar lafiya a bana, kuma wannan shi ne hari na 124 da aka kai tun daga watan Janairun 2019 kawo yanzu.