Fiye da mutum 100 ne suka mutu a wani harin tagwayen bama-bamai da aka kaddamar kan jama’ar da suka yi dandazo a kusa da kabarin Janar ɗin ƙasar Iran, Qassem Soleimani, a ranar tunawa da kisan da Amurka ta yi masa.
Tashar yaɗa labaran kasar, Irib ta ce mutum 171 ne suka ji raunuka sanadin fashewar, yayin wani jerin gwano a kusa da masallacin Saheb al-Zaman cikin birnin Kerman na kudancin ƙasar.
Tuni matakimakin gwamnan Lardin Kerman, Rahman Jalali ya bayyana wannan harin a matsayin na ta’addanci kamar yadda tashar labaran ta ruwaito.
Wani bidiyo da ya karaɗe intanet ya nuna gawawwaki da dama a kan wani titi.
Ɗaruruwan mutane ne aka ba da rahoton suna tattaki zuwa kabarin Souleimani ranar Laraba a wani ɓangare na zagayowar ranar tunawa da mutuwarsa, wanda aka kashe a wani harin jirgin Amurka maras matuƙi a ƙasar Iraqi mai maƙwabtaka a shekara ta 2020.
Ana ganin Soleimani a matsayin wani ƙusa mafi ƙarfin iko a Iran bayan Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
A matsayinsa na kwamandan Rundunar Juyin-Juya-Hali da ke kula da ayyukan dakarun Ƙudus da kuma samar makamai, kuma shi ne jami’in da ke tsara manufofin Iraƙi a faɗin yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman dari-dari a yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon yakin Isra’ila da Hamas a Zirin Gaza.
Shekaru hudu kenan da mutuwar Soleimani wanda harin na jirgin Amurka mara matuki ya kashe shi a birnin Bagdad na Iraq.
Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin da ake ganin shi ne mafi muni da aka kai wa Iran tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979.
Kodayake Isra’ila ta kai jerin hare-hare kan wasu daidaikun mutane a Iran saboda shirin nukiliyar kasar, amma ba ta taba kai hari kan taron jama’a ba.
Kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi irinsu IS sun sha kaddamar da hare-hare a baya da suka yi sanadiyar mutuwar fararen hula a yankin da mabiya akidar Shi’a ke da rinjaye a Iran.