✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tabbatar da ingantacce kuma sahihin zabe ba na Hukumar INEC kadai ba ce

Masu iya magana sun ce idan aski ya zo gaban goshi, ya fi zafi. Yayin da ya rage kwana 22, a yi babban zaben kasar…

Masu iya magana sun ce idan aski ya zo gaban goshi, ya fi zafi. Yayin da ya rage kwana 22, a yi babban zaben kasar nan da za a fara da na Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa ranar 16, ga watan gobe, tuni Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana wa duniya cewa za a yi amfani da na’urar tantance katin kada kuri’a, sannan za a gudanar da tantance masu kada kuri’a da kada kuri’ar kanta a lokaci daya, sabanin zabubbukan baya da aka rika ware lokacin tantancewa da na kada kuri’a. Tsare-tsaren da ko kusa jam’iyyun adawa ba su da ra’ayin a yi haka, abin da suka kafe a kai, shi ne lallai a zauna a kan tsohon tsarin da ke raba lokacin tantancewa da na kada kuri’a.

Haka Hukumar INEC a jihohi ta kafe cikakken jerin sunayen ’yan takarar da jam’iyyu 91, suka tsayar a zabubbukan naSshugaban Kasar da na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa. Jam’iyyu 72, suka tsayar da ’yan takarar shugabancin kasa, kuma akwai mata 28 da za su rufa wa maza a cikin takarar neman shugabancin kasar. Jam’iyyar SDP ba ta da dan takarar Shugaban Kasa ne saboda karar da ke gaban kotu da ’yan takararta biyu ke jayayya ya juna a kan wa ya cancanci a tsayar tsakanin tsohon Gwamna Donald Duke da tsohon Ministan Labarai Farfesa Jerry Gana. Hakazalika babu ’yan takarar majalisun dokokin na kasa da na jihohi har zuwa yanzu a rassan Jam’iyyar APC na jihohin Imo da Zamfara, bisa ga tashin-tashinar da aka samu a jihohin biyu a lokutan zabubbukan fitar da gwanayen da za su tsaya wa jam’iyyun a babban zabe.

A zaben na bana Hukumar INEC ta bayyana cewa za ta yi amfani da Kundin Dokar Zabe ta shekarar 2010, kasancewar har zuwa wannan lokaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa ya sa hannu a kan gyaran da ’yan Majalisar Dokoki suka yi wa dokar zaben, balle a yi amfani da su a zabubbukan bana,bisa abin da bangaren zartaswar ya yi zargin gyararrakin ba su dace da tafiyar da ake ciki ba. Ta kuma ce akwai masu kada kuri’a miliyan 84 da dubu 4 da 84, wanda shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu a tarihin kasar nan da Nahiyar Afirka baki daya, kuma yana ma cikin adadi mafi yawa na masu kada kuri’a a duniya. Akwai kuma ’yan takara 1,904 da za su fafata a neman kujerun Majalisar Dattawa 109, yayin da Majalisar Wakilai mai kujera 360, ana da yan takara 4,680, da za su fafata a junansu.

A dai wancan jerin sunayen ’yan takarar Majalisar Dokoki ta Kasa da Hukumar INEC ta fitar an yi kididdigar cewa kimanin sanatoci 41, masu ci yanzu ba su samu shiga takara mai zuwa ba, kodai a kan ba su yi nasara ba a zabubbukan fitar da ’yan takarar na jam’iyyunsu, ko sun nemi matsawa gaba  don shiga takarar gwamnoni a jihohinsu, ko kuma fargabar hadarin siyasar jihohin nasu ce ta sanya suke gudun kada su fadi ba nauyi. Wadansu kuma gajiya aka ce sun yi da siyasar baki dayanta kamar Sanata Abu Ibrahim mai wakiltar Katsina ta Kudu, yau shekara 16 da suka gabata, a Majalisar Dattawan.

Wadansu daga cikin sanatocin da ba su samu tsayawa takarar ba sun hada da tsofaffin gwamnoni irin su Sanata Bukar Abba Ibrahim na Jihar Yobe da tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tsofaffin gwamnonin jihar Filato Sanata Joshua Dariye (da yanzu ke zaman sarka bayan samunsa da Kotu ta yi da laifin yin sama-da-fadi da kudaden jama’a a lokacin yana gwamna) da Sanata Jonah Jang. Sanatoci masu ci yanzu irin su Sanata Usman Bayero Nafada daga Jihar Gwambe da Sanata Jerimiah Useni daga Jihar Filato, likkafa ce ta yi gaba inda suka samu tsaya wa jam’iyyarsu ta PDP takarar neman gwamna a jihohinsu, yayin da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa na shekara 8, Sanata Dabid Mark na PDP, shi ma a wannan karon ya kauce ba zai tsaya takarar ba daga jiharsa ta Binuwai. Gwamnonin jihohin Gombe da Yobe da Ogun da Imo da Borno da Kwara da Oyo da suke kammala wa’adinsu na zango biyu a bana, duk sun samu tsaya wa jam’iyyunsu daban-daban takarar ’yan Majalisar Dattawa a wannan karo.

A yau kuma babban abin da ’yan adawa musamman na Jam’iyyar PDP suka fi mayar da hankali a kai, shi ne nuna fargabar da cewa Hukumar INEC ba za ta gudanar da zabubbukan ba cikin kamanta gaskiya da adalci da za su tabbatar da sahihi kuma karbabben zabe, ma’ana za ta yi magudi don tabbatar da Jam’iyyar APC ta ci gaba da mulki. Zarge-zargen da Hukumar INEC da shi kansa dan takarar Shugaban Kasa a APC, Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC suke ta musantawa.

A cikin jawabinsa mai shafuffuka 16 na farkon wannan mako an ruwaito tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo (kanwa uwar-gami), yana zargin Shugaban Kasa Buhari da Mataimakinsa Farfesa Osinbajo da Hukumar INEC cewa suna ta kulla makirci iri-iri, duk da niyyar ganin lallai ko ana ha-maza, ha-mata sai APC ta ci gaba da mulkin kasar nan, bayan ranar 29 ga watan Mayun bana. Hatta masu sa ido a zaben na Kungiyar Tarayyar Turai da kungiyoyi kare mulkin dimokuradiyya da na addinai da sauran kungiyoyi irin wannan fargaba suke ta nunawa, yayin da Hukumar INEC ta dage a kan za ta gunadar da zabubbukan cikin kamanta gaskiya da adalci.

Kasashen duniya irin su Tarayyar Turai da Amurka da suka dade suna mulkin dimokuradiyya sukan sa kasashe masu tasowa irin namu gaba wajen ganin tabbatuwa da dorewar mulkin dimokuradiyya a koyaushe. Ba don komai ba  sai don shi ne mulkin jama’a da kowane dan kasa ke da ikon sa hannunsa a yi da shi, kuma shi duniya ke yayi. Saura da me? Yanzu duniya ta zura wa kasar nan da masu mulkinta da ’yan adawa da dukan ’yan kasa da ita kanta Hukumar Zabe idanu don ganin yadda zabubbukan za su kasance. Abin da ya sa na ce haka sai don kamar yadda na sha fadi a baya a cikin wannan fili cewa alhakin gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe ba wai a kan gwamnati da jam’iyyar da take kan mulki ko hukumar da ke gudanar da shi kadai ya doraga ba, a’a ya dogara ne a kan kowa da kowa, wato ma’ana kowa ya yi abin da ya dace a gani idan sahihi kuma ingantaccen zabe bai samu ba. Koke-koke da zarge-zarge ga Hukumar Zabe ko jam’iyyar da ke mulki za ta murde zabubbukan da aka fi ji daga bakunan ’yan adawa ba komai ba ne, sai don haka ’yan siyasar nahiyarmu ta Afirka suka saba yi.