✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tabarbrewar tsaro ya nuna kamar babu gwamnati ne a kasar nan – Sanata Gobir

Sanata Abdullahi Gobir mai wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa da ke neman jama’arsa su sake ba shi dama karo na biyu, ya tattauna…

Sanata Abdullahi Gobir mai wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa da ke neman jama’arsa su sake ba shi dama karo na biyu, ya tattauna da Aminiya a makon jiya kan harkokin majalisar da yanayin tsaro a kasar nan da sauransu:

Aminiya: Yaya yanayin jagoranci yake a Majalisar Dattawa a daidai lokacin da kake karshen zangon farko a majalisar?
Sanata Gobir: Ka san shi jagoranci abu ne mai wuya kuma duk wanda aka bincika ana samun matsaloli wurinsa daidai gwargwado, abin da kawai zan ce a nan zauren majalisa in kuna ciki babu nuna bambancin siyasa, koyaushe akan yi kokari kan abin da zai taimaki kasa, amma akan dan sanya muradun jam’iyya nan da can da ba a rasa ba. Kuma ba za ka yanke hukunci ka ce dari bisa dari ’yan majalisa gaba dayansu suna aiki don Allah da taimaka wa kasa ba, wasu na yi domin aljihunsu da kansu, amma in ka duba za ka ga masu yi don al’umma da kasa za su fi masu son kansu yawa.
Aminiya: Me za ka ce kan taron kasa da aka kammala kwanan nan da yanayin tsaro a kasar?
Sanata Gobir: Kan maganar taron kasa ba zan yi magana sosai a kansa ba, tunda na san dai dole za a kawo shi zauren majalisa. Ko akwai kuskure ko babu ba zance komai a kai ba, in an kawo za mu bude shi mu gudanar da adalci a kansa. Kuma ya kamata jama’a su yi mana adalci domin Shugaban kasa ne ya yanke shawarar yin wannan taron kasa kuma an aiwatar, don haka za a kawo mana kundin domin yanke hukunci. Maganar ’yan ta’adda ko mahara da suka addabi kasar nan, gaskiya an yi wa lamarin rikon sakainar kashi, kai ka ce dai ba gwamnati a kasar nan. Wannan yanayi ban taba ganinsa a rayuwata ba, rayuwar dan kasa ba ta da wata daraja ko kima a walankance take, kuma ba ruwan gwamnati, amma sai ka ji wasu mutane na fadar cewa gwamnati tana yin kaza da kaza, duk a banza. Ya kamata gwamnati in da gaske take yi kan mahara ko ’yan Boko Haram ta dauki mataki fiye da yadda ake yanzu, da maharan ke kokarin kwace wasu wurare suna sanya tutocinsu. Gaskiya yadda abubuwa ke tafiya ba abu ne mai kyau ga kasar nan ba. Misali abin kunya da ke faruwa a ce fiye da kwana 130 da sace ’yan matan Chibok amma har yanzu ba wani abu, sai maganganun shirme kawai ake yi a kansu, ba wani abu da aka yi kuma ba su fadi komai ba, ba wani mutum da zai karbi wannan matsalar, abin kunya ne ga gwamnatin kasar abin da ke faruwa a yanzu. Za ka tambayi kanka me ya sa ba mu gayyaci Shugaban kasa majalisa ba, kan wannan lamari? To mun yi abin da ya fi gayyatarsa, domin duk wanda ke da ruwa da tsaki kan harkar tsaro mun gayyace shi a zauren majalisa kuma ya zo ya ba mu bahasi, har muka gaya musu inda ake bukatar gyara da inda kasawarsu ta bayyana da matakin da muke son su dauka. Amma har yanzu ba wani canji ko matakin da aka dauka, nan ba da jimawa ba za mu dauki mataki koda na saukar da su ne gaba daya. Maganar gwamnati na iyakar kokarinta kan harkar tsaro ni ban gamsu ba, don ni dai Injiniya ne a fannin karatu, wanda ya san yanayin tsaro da daukar matakin da ya dace. Misali Allah Ya tsare a ce daya daga cikinsu an sace ’yarsa ko matarsa, zai tsaya ne har sai wani ya karbo masa ita? Ina da tabbacin in daya daga cikin manyan hafsoshin soja ko Shugaban kasa shi kansa a ce iyalinsu na cikin wadanda aka sace ba za su tsaya wannan jiran ba. Kana ganin yanzu wasu matan daga cikin wadanda aka sacen ba su da juna biyu yanzu? To haka ya dace? Shi ne ya sa na gaya maka ni ban gamsu ba, dole akwai lauje cikin nadi akwai inda matsalar take.
Aminiya: Idan mua dawo nan gida me ka yi wa jama’arka?
Sanata Gobir:To gwargwado na yi abubuwan ci gaban al’ummata a shekarata ta farko da shiga ta majalisa cikin wata daya na nemo Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya ta zo nan Sakkwato ta gyara madatsar ruwa ta Goronyo wadda an kashe mata fiye da Naiar biliyan uku. Bayan haka na kafa cibiyar koyon sana’o’i a garin Sabon Birni, sannan na sanya aka gyara gidan Sarkin Gobir da gyara matsalar wuta har muka hada kauye takwas da wutar lantarki da sauran ayyuka da dama. Kamar daukar nauyin matasa su yi karatu. Rigimar siyasar da muka shiga a Jam’iyyar PDP ya sanya muka makara ga wasu ayyuka ba mu aiwatar da su ba, sai yanzu muke kan yi, domin mun tantance su wae ne ke tare da mu su wane ne ba su tare da mu, domin gudun kada ka dauki abinka ka bayar ga wanda ba ya goyon bayanka. Kuma jama’ata su sani insha Allah zan sake tsayawa takarar kujerar Sanata a karo na biyu a zaben 2015. Abin da ya ba ni kwarin gwiwar sake tsayawa takara shi ne aikin da na soma na jama’a ban karasa ba, wato janyo wa jama’ata amfani da kuma masana’antu da nake son in aiwatar a dukkan mazabata ta Sakkwato ta Gabas. A halin yanzu mun yi tsari tare da daftarin hanyoyin da za mu bi don samun nasarar aiwatar da lamarin da zai bunkasa jama’ata, a yanzu matasa 92 ne muka samar wa aiki a ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da 42 da suka shiga aikin soja wannan aiki muna son mu ci gaba da yin sa domin taimaka wa al’umma.