Assalamu Alaikum. ‘Yan uwa yau na zo ne da wata ‘yar takaitacciyar nasiha ga iyaye da nufin samar da hanyar tsira.
Abin da ya sa na shirya wannan nasiha kuwa shi ne ganin yadda iyaye suke wasa da tarbiyar ‘ya’yansu ko kuma suke kuskure wajen yin tarbiyar.
Rashin tarbiya ce ta sa yanzu komai ya tabarbare, matasa da dama suka lalace suka balbalce. Iyaye suka gaza wajen sauke nauyin da Allah Ya dora musu, gwamnati ta zama wajen handama da baba-kere. Makarantun suka lalace, malamai suka zama jahilai kuma dalibai suna koyon jahilcin a wajensu. Wannan shi ake kira malami ya bace, kuma shi ma dalibin ya bace.
Duk abin da zayyana a sama suna da nasaba da alamun ranar karshe wato kiyama domin Manzon tsira Muhammad SAW ya mana nuni da hakan.
Matsalar a nan ita ce, sau da yawa za ka ga da ya lalace amma iyayensa ba su ma sani ba. Su a tunaninsu yaronsu yana kan hanya madaidaiciya ne saboda rashin kula, sai abin ya yi kamari kuma sai su zo suna kuka suna da-na-sani. Dama ance ice tun yana danye ake tankwara shi.
Babban abin da ke janyo tabarbarewar tarbiya a wannan zamani shi ne kwadayi da son abin duniya. Mutane da yawa suna tsoron mutuwa, amma kuma suna so su shiga Aljanna. Watarana muna zaune sai na jiyo wani mahaifi yana fadawa dansa cewa: “Ka yi karatu sosai, ka zama ma’aikaci mu ci kudin gwamnati.” Allah cikin ikonsa, maimaikon wannan yaron ya zama ma’aikaci ya sato kudin gwamnatin su ci, sai ya zama barawo a gida. Ya saci kudin mahaifin da na mahaifiyarsa da kuma mutanen gari, kuma ya zama kasaitaccen mashayi. Wannan abin ya janyo wa wannan mahaifin matsala da kyama a cikin mutane, har ya zama yana kuka. Haka kuma na taba jin wani dattijo yana fadawa jikokinsa cewa: “Ku yi karatu sosai, domin da ace na yi karatun boko, da yanzu haka da ni ake wannan sace-sacen kudin da kuke ji ana yi a Najeriya.” Ke nan yana nuna wa matasan cewa su yi karatun boko su zama barayi su saci kudin gwamnati.
Irin wannan tarbiyar da iyaye suke ba ‘ya’yansu shi ne ke janyo lalacewar komai. Maimakon irin wannan wasiyoyi da iyaye suke yi, me zai hana iyaye su rika yi wa ‘ya’yansu wasiya da jin tsoron Allah? Da nuna musu gudun duniya da taimakon al’umma? Irin wannan wasiyoyin ne manzanni da salihan bayi suka yi wa ‘ya’yansu, wanda hakan ya taimaka musu wajen sauke nauyi da ke wuyarsu na tarbiyantar da ‘ya’yan.
Haka kuma watarana ina kofar gida da misalin karfe 11 na dare, sai ga wata yarinya tana wucewa, da na tambaya sai aka ce min gida za ta tafi. Kuma tana da iyaye a gidan. Abin mamaki a nan shi ne, ya za a yi uba ya yi barci bai ga yarinyarsa ba? Irin wannan na faruwa da yawa, inda za ka ga uba bai ma san inda dansa ke kwana ba. Kawai dai ya san yana da da. Duk da cewa irin wannan matsalar ta fi yawa a wajen maza, amma yanzu haka abin ya fara yin kamari a tsakanin mata. Kuma lalacewa ta kai lalacewa ace yarinya mace tana zuwa yawo da daddare kuma ta dawo cikin dare ba tare da tana jin tsoron cewa za a mata wani abu ba a gida.
Hakanan idan ka koma bangaren shaye-shaye abin ba a cewa komai. Watarana wani abokina yake ba ni labari cewa an yi gasar shaye-shaye, amma abin mamakin shi ne yadda ya fada cewa wai mace ta lashe gasar, domin dukan wadanda suka shiga gasar sun yi mankas sun kasa tashi, amma ita ta tashi har ta fito waje. Yanzu haka maganar da ake yi daya daga cikin wadanda suka yi gasar ya haukace. Me ye amfanin irin wannan gasar?
Wani abin da ke janyo lalacewar matasa kuma shi ne, yadda iyaye suke sakaci wajen biya wa ‘ya’yansu bukatunsu. Za ka ga mahaifi ko mahaifiya suna ganin ‘ya’yansu da abin da ba su ne suka saya musu ba, kuma sun san cewa ‘ya’yan ba sana’a suke yi ba, amma su yi shiru. Wani lokacinma za ka ‘ya’yan suna taimakon iyayen da irin wannan kudin ko wani abun duniya da suka samu. Abin tambayar a nan ita ce: wai ina suka samo wannan kudin? Amsar it ace, idan mata ne, to samarinsu ne suka ba su, kuma duk yarinyar da saurayinta ke daukar nauyin al’amuranta tun kafin su yi aure, tana iya yiwuwa ya bata maka yarinya duk da cewa ana samu wadanda suke taimakawa don Allah. Kuma irin wannan abin yana sa yarinyar ta raina iyayenta. Idan kuma namiji ne, to kodai yana rokon abokanansa, ko kuma yana dauke-dauke. Idan kuwa rokon abokai yake yi, idan ba a yi sa’a ba, idan abokanan banza ne, to suna iya tunzura shi ya yi duk abin da suke so. Kodai su koya masa shaye-shaye, ko su koya masa sata.
A karshe nake tambayar iyaya: A matsayinka na uba, sau nawa ka taba tashi cikin dare ka yi addu’ar Allah Ya shiryar maka da ‘ya’yanka? Idan baka taba ba, to ka dage domin tarbiyar ‘ya’yanka dole ne, kuma Allah zai tambayeka. Kuma yanzu muna wani lokaci da tarbiya ta yi wahala. Aiki ne babba a gabanku iyaye, sai kun yi hakuri. Allah Ya baku ikon sauke wannan nauyin.
Isiyaku Muhammed ya rubuta wannan makala. Kuma za a iya samunsa a wayar tarho: 07036223691