Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce akalla mutane miliyan 146 ne ke rasuwa a duk shekara sakamakon cututtuka masu alaka da shan taba sigari.
Daraktar hukumar a Nahiyar Afirka, Matshidiso Moeti ce ta bayyana hakan yayin wani taro ta yanar gizo da hukumar ta shirya ranar Alhamis.
A cewarta, yawan matasa ’yan kasa da shekara 20 masu shan taba sigari a nahiyar ya karu; ta yadda a duk cikin matasa biyar, ana samun daya da ke shan sigarin.
Daraktar ta kuma ce, “Mutum miliyan 1.2 ne ke rasuwa a duk shekara a fadin duniya, sakamakon zukar hayakin tabar sigari da ake sha a kusa da su a nahiyar Afirka.”
Dokta Moeti ta koka kan karuwar amfani da dangogin taba sigari kamar shisha da sauransu a Afirka.
Ta cewa shan taba sigari na kashe kusan daukacin sassan jikin dan Adam.
A cewarta, zukar taba sigari na daga cikin manyan abubuwan da suka fi kashe mutane a duniya wadanda da za a iya kauce wa.
Jami’ar ta WHO ta ce daina shan sigari ita ce babbar hanyar kauce wa kamuwa da cutar kansa, ciwon zuciya, shanyewar barin jiki da sauransu.
Misis Moeti ta kara da cewa, “Ana iya ganin daina shan sigari abu ne mai wuya, amma gara mutum ya fara; Ya yanke shawarar yin rayuwar da shi ke jan ragamarta, ba ya zama sigari ke jan akalarsa ba.
“Ana iya cewa da wuya, amma gara mutum ya dauki mataki yanzu, kafin daga baya ya kamu da matsalolin rashin lafiya ko ma mutuwa,” a cewar Dokta Moeti.