✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta’aziyyar Indon Musawa

Wadannan na cikin da wakar da marigayi Shata ya yi wa marigayiya Indon Musawa

“Wata ’yar yarinya, mai kyan diri da kyan tsari.

“Ta yi zaune kamar Kumsa, ta dan karkace kamar Rufu’a

“Mai da in fadi kamar Ba Sim Lallam Ha-kuri”.

Wadannan na daga cikin kalaman da marigayi Dokta Mamman Shata ya yi wa marigayiya Hajiya Indon Musawa a cikin wakar da ya yi mata.

’Yar qabilar Fulani, an haifi Indon Musawa ne a garin Danzabuwa da ke Karamar Hukumar Tsayawa a Jahar Kano kimanin shekara 77 zuwa 78 da suka gabata.

Mahaifiyarta ’yar salin Zangon Daura ce yayin da mahaifinta dan garin Rimi ne, duk dake Jihar Katsina.

An yi wa Indo auren farko a garin na Zango amma bata zauna ba. Sai kuma ta sake yin wani auren a gidan Galadiman Kazaure, inda har ma ta haihu a can, amma ta sake fita inda ta nufo Musawa gidan kanen mahaifiyarta, Galadiman Kurkujan Alhaji Usman Danbaba tana dauke da waccan igiyar auren ta Kazaure.

Anan kuma gidan Galadiman Kurkujan Shata ya ganta kuma ya nuna yana son ta amma ba tare da ya san tana da aure ba.

Shata ya zo zance na farko tare da dan rakiya kuma dan jagoransa da ake kira Musa na Amare, amma ziyarar da bata zo masu da dadi ba domin Galadima Usman ya fito yana fada akan cewa ta yaya maroki zai zo gidan sarauta neman diyar gidan bayan kuma tana da aure?

Ji da kuma ganin yadda Galadima ya fito ya sa shi Shatan ya sulale ya bar Na Amare da karbar hukunci, domin sai da aka ci shi tarar Fam biyar.

Shata da Indo basu sake haduwa ba sai a Katsina a tsakanin shekara ta 1957 zuwa 1958.

Indo ta tarar da Shata a unguwar ’Yar aduwa inda yake wani wasa.

Ganinta yasa ya tambaye ta abin da ya kawo ta, nan ta ce mashi ai tana nan Katsina, gudowa ta yi. Anan ne Shata ya fara yi mata wannan waka ta Indon Musawa.

Kazalika, Indo ta yi aure a Katsina ta auri mahaifinsu Usaini, wato, Alhaji Ibrahim.

Indon Musawa ta koma garin Sandamu da zama inda Allah ya karbi rayuwarta a daren Alhamis, 10 ga watan Mayu, 2021.

Wato, Indo ta sakko a cikin sunduki a ranar Juma’a inji Shata, sannan ta koma a cikin Makara a ranar Juma’a.

Har ila yau, kafin rasuwar ta, Allah ya jarabci Indon Musawa da rashin yin magana bayan komawarta garin Sandamu don jinyar wani dan uwanta wanda daga karshe ta yanke shawarar zama a can, maimakon zuwa da dawowa.

Kamar yadda yayanta kuma wanda ta taso a hannunsa, Malam Usaini Ibrahim ya ce, ta samu waccan matsala ta rashin yin magana amma kuma tana jin duk abin da ake fadi.

“Wata rana ta fita zuwa wani wuri, to akan hanyar ta ta dawowa gida ta fadi kasa, daga nan sai maganar ta dauke. Babban abin da ke fitowa bakin ta shi ne, ‘Allah ko? Allah’,” inji shi.

Indon Musawa dai ta rasu ta bar ’ya’ya hudu a duniya; uku maza, daya mace wacce ake kira da A’isha.