✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyyar Fadar Bege

Assalamu alaikum, Editan Aminiya ka ba mu dama, mu mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan marigayi Umar Abdul’Aziz Baba Fadar Bege, da kuma Imamul Shu’ara’in nabi…

Assalamu alaikum, Editan Aminiya ka ba mu dama, mu mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan marigayi Umar Abdul’Aziz Baba Fadar Bege, da kuma Imamul Shu’ara’in nabi Sharif Rabi’u Usman Baba da kuma malaminsa Assayadi Sharu Sani . Allah ya ba ku ikon jurewa. Shi kuma Allah Ya gafarta masa; mu kuma idan tamu ta zo Allah Yasa mu cika da imani. Daga alyasa’u Haruna Imam Ningi, Jihar Bauchi. 08058624152 da Jibrin Aliyu Badawa U/gaya Kano 08095655514 da Ibrahim Mai Kayan miya Ningi 08070865097.

Sakonnin waya

Ga Ummu dankwambo
Farar uwa mai share hawayen matan Jihar Gombe, ina mika sakon barka da sallah gareki. Allah ya maimaita mana. Daga Ummu AbdulBasid, Gombe 08125518587.

Ga kukan Akoti da Janjala
Shugaban karamar Hukumar Kagarko, Mista Akuso Yusuf danjuma, mutanen Akoti da Janjala sun yi maka laifi ne? Ka ki kammala musu aikin wutar lantarki, amma ka kammala na garuruwan Kenyi da Shadalafi da Kurmin Dangana. Don Allah a rika adalci. Daga Hussaini Umar Akoti. 08054547165.

Masallacin Sultan Bello na Musulmi ne
Edita kowane Musulmi na da hakki a Masallacin Sultan Bello, don haka muke son a rika yin Maulidin kasa a cikinsa. Kuma kada wata kungiya ta rika cewa wannan masallaci mallakinta ne. Mabiya darikun sufaye ku bi hanyar lalama ta yadda za mu cimma wannan buri, tunda muna da hakki a ciki. Allah Ya yi mana muwafaka. Daga Sham’unu Sheikh Ali Musa Gabari. 08035837847.

Allah ya sauya mana PDP
Salam Aminiya ku gaya wa ’yan PDP motar da suke ciki tayar ta kusa fashewa, da ma direban dan koyo ne; a daidai gada za ta fashe. Ka ga sai cikin ruwa. Shi ke nan mun huta. Allah Ya yi mana sauyi mai amfani. Amin. Daga Adamu Suleiman Kaugama 08057672400.

Ga kukan Shakato
Al’ummar garin Shakato da ke karamar Hukumar K/Hausa ta Jihar Jigawa na kukan rashin ababen more jin dadin rayuwa. Domin shugabannin karamar hukumar sun mayar da mu ’ya’yan bora. Ba mu da wutar lantarki, hanyarmu ta lalace ga kasuwarmu. Daga Iliyasu Muhammad Shakato K/Hausa, Jihar Jigawa 07083380322/08147208892.

Ga M.J Al-Mustapha
Mu matasa na Arewa muna so ka wakilce mu a taron kasa da za a yi. Mun gode. Daga Suleiman Feleke, Makarfi 07039626175.

Ga Ali Nuhu
Don Allah Edita ka isar da sakona ga Ali Nuhu kan ya ji tsoron Allah a duk inda yake. Daga Maryam Abdullahi 07010992699.

Ga Kabiru Sani Kwangila
Edita don Allah ina son ka isar da godiyata ga Kabiru Sani Kwangila, bisa daukar nauyin shirin Tambaya Mabudin Ilimi da yake yi. Don Allah ya dauka har da Jihar Sakkwato, don suna bukatar shirye-shirye irin wadannan. Daga Amina Muhammad 08030723596.

Barka da sallah
Assalamu alaikum. Al’ummar Musulmi da fatan an yi sallah lafiya. Allah Ya maimaita mana amin, summa amin. Daga Suleiman SBK 07038999155.

Ga Bamanga Tukur
Assalamu alaikum, Aminiya haba Bamanga Tukur ka kare mutuncinka da na iyalanka, saboda ka nuna gwanda ka kare mutuncin Goodluck, ya fi ka kare mutuncin Arewa. Kuma ka sani PDP masu shi ne suka kwashe kayansu, domin Atiku da Sule Lamido da Kwankwaso suna gabanka a rashin kunya da iya siyasa. Daga Alhaji Sale Zazzaga, Jos Bukuru 08036345317.

’Yan Najeriya ga Al-Mustapha 2015
Zuwa ga ’yan Najeriya maza da mata, wata dama ce ta same mu ta fitowar Manjo Hamza al-Mustapha. Ya kamata mu zage damtse mu zabe shi a amtsayin shugaban kasa a shekarar 2015. Daga Sameera Bello Abdullahi Sakkwato 08107412275.

Ga Farfesa Jerry Gana
Mu dai a saninmu, ba mu san Jerry Gana a matsayin Shugaban yankin tsakiya ba, wato ‘Middle Belt’ a Turancin Ingilishi. Idan kuwa shi ne, to a ina aka nada shi? Daga 08059439045.

Barka da Sallah
Assalamu alaikum. Bayan haka barka da sallah da fatan alheri. Allah Ya karbi ibadunmu. Allahumma amin. Daga Lameenu Aleeyu Ladan G/Bore. 08095187562.

Masu kudi ku aurar da zawara
Yadda Hisba ta soma aurar da zawarawa a Kano, da masu kudin Kano za su kwaikwaya da an kara rage marasa aure. Daga Bello Kano 08162453996.

Ga Gwamna Kwankwaso
Aminiya ya kamata ku mika min gaisuwa ga Gwamnan Kano, Injiniya Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso. Daga Bashir Soja Dala Kano 08106631268.

Aminiya ba ta wuce ni
Gaba dai-gaba dai jaridar Aminiya, duk mako ba kya wuce ni. Ina so in zama daya daga cikin masu karatunki. Daga Khadija A. Amir Kano 07031380370.
Ina amfanin Hukumar NOA?
Mu ba mu san amfanin Hukumar Wayar da Kai ta kasa NOA a kauyuka ba. kauyuka na bukatar wayar da kai fiye da ’yan “GATA” na birni. Na kauye an maida su “JAKUNA” Allah gatan bawa. Daga Hassan Ibrahim Ningi, Jihar Bauchi. 07085622919.

’Yan mata ke yaudara
Salamun alaikum. Aminiya ku ba ni dama in mayar da martani ga ’yan matan da ke cewa samari mayaudara ne. Idan aka duba za a ga mafi akasarin yaudarar daga ’yan mata ne. Daga AbdulMalik Shu’aibu Kanoma 07062319080.