Assalamu alaikum Aminiya. Na shigo wannan fili ne domin na mika sakon ta‘aziyyata ga dukkan a’lummar Musulmin duniya, dangane da al’ummar Musulmin da suka rasa rayukansu Sakamakon ruftawar na‘urar daukar kaya a Masallacin Harami da ke kasar Saudiyya.
Hakika wannan wani babban rashi ne da duniya ba za ta taba mancewa da shi ba. Da wannan nake addu’ar Allah ya jikansu ya gafarta musu, ya sa Aljanna ta zama makoma garesu. Wadanda kuma suka jikkata Allah ya ba su lafiya, idan tamu ta zo Ya sa mu cika da Imani. Da fatan Allah ya dauki rayuwarmu, cikin irin wannan hali muna masu bauta masa.
Daga: Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382.