✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyyar A’isha Lemu: An yi rashin kundin ilimi

A ranar Asabar da ta gabata ce Allah Ya yi wa Hajiya A’isha Bridget Lemu rasuwa tana da shekara 79, bayan ta yi fama da…

A ranar Asabar da ta gabata ce Allah Ya yi wa Hajiya A’isha Bridget Lemu rasuwa tana da shekara 79, bayan ta yi fama da gajeruwar jinya. Babban danta Nurudeen Ahmed Lemu ne ya fitar da sanarwar da ta bayyana rasuwarta a Minna.

Kuma an yi jana’izarta a ranar Lahadin da ta gabata Minna na Jihar Neja.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiya A’isha Lemu, a wani sako da Kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar inda Shugaba Buhari ya nuna jimaminsa bisa abin da ya kira “Babban rashi ne da muka yi na kundin ilimi mai muhimmanci wanda ba ya misaltuwa.”

Shugaban ya ce, “Aisha Lemu ta yi fice idan aka dubi cewa karbar Musulunci ta yi daga baya, kuma Baturiya ce, amma ta tashi tsaye domin haskaka duhun jahilci ta hanyar amfani da hasken Musulunci.”

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya ziyarci  mijin marigayiyar Sheikh Ahmed Lemu a gidansa tare da Mataimakinsa domin mika sakon ta’aziyyar al’ummar jihar Neja gare shi.

Gwamnan ya ce marigayiya A’isha ta kasance mace tagari abar koyi a Musulunci, wadda kuma ta tsaya bisa tafarkin samar wa mata ilimi domin inganta rayuwarsu.

An haifi marigayiya Bridget A’isha a garin Poole na yankin Dorset na kasar Ingila a 1940. Tana da shekara 13 ta fara tunanin sauya addininta, inda ta fara da nazarin addinan Hindu da na Bhudda amma ba su gamsar da ita ba.

Ta yi karatun jami’a a makarantar koyon al’adu da harsunan kasar Sin da na Afirka a Jami’ar Landan (SOAS), inda ta karanta tarihi da al’adu da kuma harshen kasar Sin.

A jami’ar ce kuma ta fara haduwa da dalibai Musulmi wadanda suka rika ba ta litattafan addinin Musulunci, kuma ba da dadewa ba sai ta musulunta a 1961, lokacin tana shekararta ta farko a jami’ar.

A lokacin ne ta bayar da gudunmawarta wajen kafa kungiyar dalibai Musulmi na makarantar ta SOAS a Jami’ar Landan, kuma ita ce Sakatariyar Kungiyar ta farko.

Bayan ta kammala karatun digiri na farko a jami’ar Landan, sai A’isha Lemu ta koma karatun digiri na biyu a kan harshen Ingilishi, kuma a lokacin ne ta fara ganin Sheikh Ahmed Lemu, wanda shi kuma ya isa Landan ne domin karo ilimi a Jam’iar Landan.

Bayan kammala digirinta na biyu sai ta koma Kano a 1966, inda ta fara koyarwa a Makarantar Nazarin Larabci, a lokacin da Sheikh Ahmed Lemu ke shugabantar makarantar.

An daura mata aure da Ahmed Lemu a watan Afrilun 1968, inda Aisha ta kasance matarsa ta biyu. Ta tafi Sakkwato domin kama aiki a matsayin shugabar makarantar mata ta gwamnati.

Daga baya ta koma Jihar Neja bayan da aka kirkiri jihar daga jihar Arewa maso Yamma a 1976, kuma ta zama shugabar Makarantar Horar da Malamai Mata ta Minna har 1978.

Ita da mijinta sun kafa Gidauniyar Ilimin Musulnci (IET), kuma ita ta kafa Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) a 1985.