✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyya ga Media Trust

Ina son mika ta’aziyyata ga daukacin mutanen gidan wannan jarida mai farin jinni, wato Dailytrust da Aminiya da iyalan Marigayi, Suleiman Muhammad da ’yan uwa…

Ina son mika ta’aziyyata ga daukacin mutanen gidan wannan jarida mai farin jinni, wato Dailytrust da Aminiya da iyalan Marigayi, Suleiman Muhammad da ’yan uwa da abokan arziki. Allah Ubangiji Ya yi wa Malam Suleman Muhamamd gafara, Yasa ya huta; kuma aljanna ta zamo makoma a gareshi.
Allah Ya jikan kanen Shugaban Media Trust, Alhaji Abubakar Abdullahi Yusuf da mataimakin shugaban kungiyar Izala, Alhaji Ibrahim Muhammad. Allah Ya gafarta musu. Amin. Daga Ilyas Idris Fahad Suleja. 08030777041 da Bashir Sani Abuja 08186639204.

Sakonnin waya

Najeriya ta Kwankwaso ce
Najeriya 2015 ta Kwankwaso ce. A ba mu a huta. Daga abdulkadir Abba Suleman dangoro 08153027115.

Direbobin motar haya
Ga sakona nan ga direbobi, don Allah in sun shigo gari ko ko kuma inda mota take sauke fasinja, ko daukarsu su rika isa gun a hankali, saboda wani zai tsallaka titin ba tare da ya duba ba; wani mai mantuwa ne; wani kuwa tunanin wata damuwa yake yi. Idan direbobi suka kiyaye komai zai zo da sauki, Allah Ya karemu. Daga Malam Malam Mai zanen Hula Gololo 08032822433.

A yi wa Nafisa afuwa
Assalamu alaikum, Aminiya mai alfarma don Allah ku mika min sakona zuwa ga Hukumar Tace Fina-finai a yi wa Nafisa Abdullahi afuwa, saboda ita nake kallon fim din Hausa. Daga Musa Mai arsenal Somaila 08038001277.

Labarin Kazallah
A shafin Aminiya na ranar 14/6/13, a karkashin waiwaye kun bayar da labarin Kazallah. Na ji matukar dadin labarin. Kuma ni ma zan ba ku labarin jaruman mayaka a Jihar Bauchi, wadanda suka daga darajar masarautar. Idan kuna da sha’awa zan iya ba ku har da hotuna. Daga 08035799739.

Ga sarkin Kano
Assalamu alaikum Edita don Allah ka mika min sakon taya murna zuwa ga  Sarkin Akno, day a yi bikin cika shekara 50 a kan gadon mulki. Allah Ya kara wa sarki lafiya. Daga Asma’u Khamees Kawo, Kano 07064262451.

Edita ko ban iya Hausa ba?
Assalamu alaikum. Wai me yasa ba ka rubuta sakona, ko ban iya Hausa ba ne, ko ana biyanka ne? Daga Muhammad Abubakar Bauchi. 07067540950.

Shawara ga matasa
Aminiya ku ba ni dama in kara yin kira ga daukacin matasanmu a kan matsalar shaye-shaye da ke addabar wasu daga cikinmu. Kamata ya yi a nemi sana’a komai kankantarta; a daina zaman kashe wando; sannan a kula da ibada, tare da bin hani da umarnin Allah. Da fatan Allah ya taimake mu a min. Daga Ibrahim KSD 08031944943

Gara mulkin soja
Salam Aminiya barka da warhaka. Gara mulkin soja da halin da muke ciki. Don haka ina mana fatan Allah Ya yi mana zabin mulkin da ya fi dacewa da al’ummar kasr nan. Mulkin farar hula ya ishe ni. ’Yan arewa sun shiga halin ha’ula’i. Allah Ya sama mana mafita. Daga Jamila Fagge Mazauniyar Neja Mekunkile 08061528267.

Fatan alheri ga Aminiya
Allah Ya daga darajar wannan gidan jarida, Ya sanya albarkaSa akai. Allah Ya akre ku daga sharrin masu sharri. Daga Ummi dahiru, filin Aminu Yusuf Bakinm Kogi 08148641341.

Ga ’yan Majalisar Jihar Bauchi
Assalamu alaikum, Aminiya kui mika mini sako ga ’yan Majalisar Jihar Bauchi, Su tsaya a tsaye wajen nema wa malaman makaranta hakkinsu a wajen Abdullahi Dabo. Daga Ibrahim Mai kayan Miya Ningi 08070865097.

Ga masu daukar amarya
Aminiya don Allah ku yi kira ga samari amsu daukar amarya da su yi wa Allah, su daina. Wasa da rayukan jama’a gudu da abin hawa yayin duakar amarya ba shi ne nuna farinciki ba. Addu’a ta fi komai. Daga Aisha Kabir Jos 08180210250.

korafin buga sako
Edita ni dai Aminiyar Aminiya ce. Don Allah-Allah nike yi Juma’a ta zagayo don in smau abokiyar hira, amma ban taba turo sako ba. Don naji ana korafin ko an turo ba a bugawa, idan ba na Katsinawa ba ne. Allah Ya sa in smau shiga. Daga Jamilan Umar tunga Minna 07030891275.

A dawo da Dausayin kauna
Assalam. Aminiya don Allah ku daure ku dawo mana da filin dausayin kauna. Daga Maman Farida Dabai 08065548480.

A dawo da dausayin kauna
Edita saboda dausayin kauna nike karanta Aminiya. Don haka nike rokon  a dawo da wannan fili. Daga Sani I.G KAtsina 08182898889.

Akwai son rai a harkar ilimi
Matukar Gwamanti ba ta cire son zuciya a ahrkar ilimi, to ba za a samu ci gaban ilimi ba a Najeriya, musamman a arewacin Najeriya. Dubi yadda dalibai ke kukan faduwa jarawa (SSCE da NECO)., amma babu wani amtaki da gwamanti ta dauka. Saboda ba  ‘’ya’yan shugabanni ke zuw amakarantu ba; si wadanda bas u da galihu. Allah ya ba mu gwamnatin da za t aba mu ilimi kyauta. Daga Kabiru (KB) Sakkwato 08154872959.

Ga Gwamnan Zamfara
Gaisuwa da fatan alheri zuwa ga Gwamnan Jihar Zamfara, katafila sarkin aiki. Kuma ina gaida dukkan ma’aikatan Aminiya Daga Fatima Gusau 08124465599.

APC muna tare da ku
Jam’iyyar APC muna tayaku murna da hadewarku. Allah Ya kara daidaita ku. Allah Ya ba mu nasarar zaben 2015. Daga Sani Abdu Beta 07068223015

Ga Gwamnonin PDP
Assalamu alaikum Aminiya ya kamata gwamnonin da suke son su koma jam’iyyar APC daga PDP susan ko da su, ko ba su APC ba za ta iya kafa gwamnati a Najeriya ba. Saboda wadanda suke gun ba cikakkun ’yan siyasa ba ne. Daga Alhaji Sale Zazzaga, Jos Bukuru Najeriya. 08144406080.

Ga Ministar ruwa
Assalamu alaikum. Don Allah Editan Aminiya a gaya wa Ministar Ruwa cewa fa ba man fetur ake smau a rijiyar burtsatse ba, ruwane kawai, wanda Allah Ya adana da kanSa. Daga Kamal AbdurRasheed Sani Jaji 08059722840.

Ga takobin Shema
Edita don girman Allah ka ba ni dama in yi yabo ga Alhaji Umar Sama’ila (Takobin Shema), sboda bunkasa ilimin addini da na boko da yake yi a kowane lungu na karamar Hukumar Bakori, ta hanyar bayar da kayan aiki; da daukar ma’aikata; aiwatar da sababbin dabarun koyarwa na zamani, don cimma muradun karni. Tur amalamai karo karatu da yin adalci ga kowa, kamar yadda ya koya wurin su Maigirma Atta Oja Igala da Shugaban Hukumar Ilimin Bai daya, Alhaji Sulaimanj Dikko. Mun gode. Allah Ya yi muku jagora. Amin. Daga Amiru Isah Bakori 08075959086.

Ga Sarkin Kano
Edita ina so ka isar mini da sakon taya murna tare da godiyar Allah, bisa cikar sarkinmu, ubanmu mai kaunarmu mai kishin Jihar Kano da ’ya’yanta, Matimartaba, Dokta Alhaji ado Abdullahi Bayero, shekaru 83 da haihuwa, kuma shekaru 50 a kujerar mulkin Kano. Allah Ya ja ran Sarki. Daga Khamis Imam Kano 08030932677.