✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’addanci: Abokan Bello Turji sun ƙi amsa laifi a kotu

Mutanen da Gwamnati ta gurfanar a kotu kan aikata ta’addanci tare da Bello Turji sun musanta zargin da ake musu.

Mutanen da Gwamnati ta gurfanar a kotu kan aikata ta’addanci tare da Bello Turji sun musanta zargin da ake musu.

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar Musa Muhammad Kamarawa; Abubakar Hashimu wanda aka fi sani da Doctor; Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma ne a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne a cikin mutun takwas.

Sauran su ne jagoran ’yan ta’adda Bello Turji da wasu mutum uku da ake nema ruwa a jallo.

Ana tuhumar Bello Turji da sauran mutum bakwai ɗin ne da aikata laifuka 11 da suka shafi ta’addanci.

Duk da cewa sunayen mutum takwas aka gabatar a kotu, mutum uku ne suka hallara sauran kuma ana neman su ruwa a jallo.

Daga farko sunayen mutum huɗu lauyan gwamnati, David Kaswe, ya gabatar a matsayin waɗanda za su hallara, amma ko da alkali ya tambaye shi ina ma huɗunsu, sai lauyan ya bayar da haƙuri cewa na huɗun ana neman shi ruwa a jallo.

Bayan gabatar musu da tuhumar da ake musu, wadanda ake zargin sun musanta aikata ba daidai ba.