✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta sayar da ‘yarta a Naira dubu 600 domin ta sayi wayar salula

Sashen rundunar ‘yan sandan jihar Imo da ke yaki da masu aikata fashi da makami ta ce, a kama wata mata mai suna Nneka Donatus,…

Sashen rundunar ‘yan sandan jihar Imo da ke yaki da masu aikata fashi da makami ta ce, a kama wata mata mai suna Nneka Donatus, mai kimanin shekara 27 bisa zarginta da sayar da ‘yarta mai kwana daya da haihuwa a kauyen Ezinachi da ke karamar hukumar Okigwe jihar Imo.

Donatus da abokan huldar ta Ujunwa Udechukwu da ke aiki a ma`iakatar harkoki da walwala ta mata mai shekara 40 da kuma Nneoma Onwusereaka shekara 37 sun hada baki da uwar yarinyar suka  sayarwa wasu ma’aurata da ke neman haihuwa basu samu ba.

‘Yan sanda sun sanar da cewa, wadda ake zargi da yunkurin sayar da jaririyar ta ta ‘yar kwana daya ta gayawa ‘yan sanda cewa, ta yi haka ne domin ta sayi wayar salula da kudin sauran canjin kuma ta sayi zannuwa dasu. Nneka Donatus ta shaidawa manema labarai a harabar ofishin ‘yan sandan jihar Imo da ke Owerri ce wa, “Na sayi wayar salula ne da kudin wasu kuma na sayi zannuwa dasu da kuma takalma, dama ni burina idan na haihu lafiya in sayar da abin da na haifa domin ni bani da niyyar rike abin da na haifa ina laifi ‘ya’ya biyar nake dasu duk da wanda na sayar cikon na shida”, in ji ta.

Nneka matar da ta sayar da ‘yarta ta ce, “Na sayar da ‘yata kan kudi Naira dubu 600 na yi amfani da dubu 15 na sayi wayar salula, zannuwa da kuma takalma da sauran canjin na shiga mota na dawo gida na kirga sauran kudin na ba Nneoma Onwusereka ragowar kudin domin su fara kasuwanci da shi. Mijin matar da aka ce an basu kudi su yi sana’a ya ce, shi dai ya san an bashi Naira dubu 10 cikin kudin saboda rawar da ya taka wajen sayar da jaririyar amma ba wasu kudin azo a gani aka bashi ba. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Rabi’u Ladodo ya tabbatarwa manema labarai da aukuwar hakan ya ce, ana nan ana binciken su da zarar sun gama bincike kotu za’a tura su.