✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta lakada wa dan kishiya duka har ya mutu

Ta yi wa dan kishiyarta mai shekara bakwai dukan kawo wuka har sai da ya ce ga garinku

Wata mata mai kimanin shekara 29 ta shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin lakada wa dan kishiyarta mai shekaru bakwai dukan kawo-wuka har ya mutu.

Hukumar Yaki da Fataucin Jama’a ta Kasa (NAPTIP) shiyyar Kano ce ta cafke matar ta damka ta hannun ’yan sanda domin bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kuliya.

Daraktan hukumar a shiyyar Kano, Shehu Umar, “Mun samu labarin kisan yaron da a watannin baya aka kubutar da shi daga hannun matar.

“Da jin labarin ne jami’anmu suka bazama tare da cafke ta,” inji jami’in na NAPTIP.

Ya ce tun da farko sai da suka gayyaci wadda ake zargin zuwa ofishin NAPTIP kan zargin cin zarafin yaron da ta yi sanadiyyar rasuwar tasa.

Shehu ya ce a ranar Alhamis aka cafke matar bayan ta yi sanadiyyar rasuwar yaron a gidansu da ke kusa da kasuwar Tarauni a cikin birnin Kano.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an mika wacce ake zargin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin fadada bincike.