✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta yi wa kishiyarta duka da tabarya, ta cinna mata wuta

Ta gayyato danginta suka yi wa amaryar rubdugu, kwana 55 bayan daurin aure

Wata mata ta lakada wa kishiyarta duka da tabarya har sai da ta mutu sannan ta kona gawarta kurmus a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Kishiyar tare da kannenta dauke da tabarya ne suka yi wa mamaciyar rubdugu, suka yi mata lugude, har ta bar duniya, kwana 55 da daura auren marigayiyar Fatima da mijinta.

“Sun raba kanta biyu sannan suka sanya ta cikin daki suka banka wuta ta kone kurmus,” inji wani dan uwan marigayiyar mai suna Malam Jamilu.

Rahotanni sun bayyana cewa kishiyoyin biyu ba a gida daya suke zama ba, amma uwargidar ta yi wa marigayiya Fatima takakkiya har gida, ta yi mata bugun dawa, ta kulle ta a daki, sannan ta  cinna wa gidan wuta.

Makusantanta sun bayyana cewa, “Ba a gida daya suke zama ba, amma saboda zafin kishi uwargidanta ta kai mata takakkiya har gida.”

Malam Jamilu ya ce, “Tun karfe 10 na safe zuwa daya na rana duk mun yi magana da ita.

“Amma daga karfe 3 zuwa 4 na yammci mummunan labari mai kada zuciya da hanta wanda ba zan taba mantawa da shi ba har karshen rayuwata ya same ni cewa uwargidan Fatima ta hadu da kannenta sun yi mata dukan tsiya da tabarya.”

Marigayiya Fatima a lokacin bikinta a watan Janairu, 2021.

Marigayiya Fatima wacce zaman aure ne ya kai ta jihar Neja, ’yar asalin Sabuwar Unguwa ce da ke birnin Katsinan Dikko.

An mayar da gawar mamaciyar Jihar Katsina inda za a yi jana’izarta ranar Laraba a Sabuwar Unguwa wurin Gadar Nayelli da ke Katsina.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto jami’an tsaro ba su komai ba game da lamarin.