Wata ’yar kasuwa ta gurfana a gaban kotu saboda zargin cizon wata mata mai suna Cordelia Chiwuoba a kunne.
’Yan sanda na zargi matar mai zama a a yankin Yamco Ayobo da laifuka biyu da suka hada da cin zarafi da keta haddi amma ta musanta zargin.
- Wata mata ta cirewa kishiyarta kunne da cizo
- Ta gatsawa mai gidan abinci cizo a kunne kan rashin iya aikin
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Benson Emuerhi, ya shaida wa Kotun Majistare da ke zamanta a Ikeja, Jihar Legas cewa wadda ake zargin ta ta ciji kunnen Cordelia ne yayin wata takaddama da ta kaure a tsakaninsu.
ASP Benson ya Cordelia sa samu mummunan rauni na har abada a kunne sakamon cizon da wadda ake tuhuma ta yi mata a ranar ranar 17 ga Satumba, 2020, a gidanta..
Ya ce laifin ya saba da sassa na 168 da 173 na Kundin Manyan Laifukan Jihar Legas 2015.
Dokar ta tanadi hukuncin daurin shekara uku a kurkuku ga duk wanda aka tabbatar ya aikata laifin.
Alkalin kotun, Mai Shari’a J. A Adegun ya bayar da belin wadda ake zargin a kan N100,000 da kuma mutum biyu da za su tsaya mata.
Daga nan ya dage zaman har zuwa 10 ga watan Nuwamba domin ci gaba da sauaraon shari’ar.