✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta daba wa dan uwanta wuka bayan sa’insa a tsakaninsu

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya samo asali ne bayan wata sa’insa da ta barke a tsakaninsu

Wata budurwa mai kimanin shekaru 18 da haihuwa ’yar asalin Igbokada a Karamar Hukumar Ilaje dake jihar Ondo, Idowu Biletiri ta dabawa yayanta mai suna Kehinde Biletiri wuka har sai da ya ce ga garinku nan.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya samo asali ne bayan wata sa’insa da ta barke a tsakaninsu bayan marigayin ya tambaye ta a inda take kwana a ’yan kwanakin da suka gabata.

Idowu dai ta shafe kwanaki ba ta kwana a gida, dalilin ma da ya yayan nata ya titsiyeta bayan dawowar tata domin jin inda ta shiga tun bayan tafiyarta kafin daga bisani ya gamu da ajalin nasa.

Wata majiya a yankin da lamarin ya faru ta ce, “A maimakon wacce ake zargin ta ba dan uwan nata amsa, kawai sai ta bige da sa’insa da shi. Ana tsaka da hakan ne kawai sai ta shiga dakin girki ta dauko wuka ta daba masa. Su biyu ne kawai a gidan lokacin da lamarin ya faru.”

Majiyar ta kuma ce daga bisani an kama wacce ake zargin sannan aka damka ta hannun ofishin ’yan sanda dake Igbokada.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, Mista Tee Leo-Ikoro ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni suka fara bincike a kai.