Kwamishiniyar Harkokin Mata a Jihar Zamfara, Hajiya Rabi Shinkafi, ta ce ta ajiye mukaminta domin karbar wani mukamin na Kwamishina a Jihar Imo.
A zantawarta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara ranar Alhamis, Hajiya Rabi ta ce tan yanke shawarar yin aiki ne da gwamnatin Gwamna Hope Uzodinma na Imo.
- Sojoji sun gano matatu 14 da ke tace mai ba bisa ka’ida ba a Neja Delta
- Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Tunisia daurin shekara 4 a gidan yari
Ta ce, “Na ajiye mukamina ne na Kwamishina a Zamfara saboda na sami damar karbar wani mukamin a Imo. Ina matukar godiya ga Gwamna Matwalle da matarsa, Hajiya Aisha Matawalle, saboda kokarinsu da kuma ba ni damar yin aiki a Jihar Zamfara a matakai daban-daban.
“Dukkan rade-radin da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani akan ajiye mukamina ba gaskiya ba ne, kawai aikin masu yunkurin tayar da zaune tsaye ne,” inji ta.
Ta kara da cewa, “Ina da kyakkyawar alaka da Gwamna da kuma mai dakinsa, ina daukarsu a matsayin ’yan uwana, kuma haka zan ci gaba da kallonsu har na tafi Imo.
“Da Gwamna Matawalle da Uzodinma dukkansu sun tattauna batun sannan sun amince a matsayinsu na ’yan jam’iyya daya kuma abokan juna,” inji Hajiya Rabi Shinkafi. (NAN)