✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Syria: Sanyi na kashe jarirai daidai lokacin da yaki ke zafafa a Idlib

A filin Allah kuma cikin tsananin hunturu, Mustafa Hamadi da iyalansa suka zauna cikin wani tanti da ke kauyen Killi, a Arewa maso Yammacin yankin Idlib…

A filin Allah kuma cikin tsananin hunturu, Mustafa Hamadi da iyalansa suka zauna cikin wani tanti da ke kauyen Killi, a Arewa maso Yammacin yankin Idlib na kasar Syria, wanda shi ne matsuguninsu na biyu kasa da shekara daya. Sanyin da aka yi na kasa da maki daya a daren ranar 11 ga Fabrairu ya sanya su kwana ido bude, sai dai kafin daren ya raba tsakiya, Mustafa ya shigar da tukunyar gas cikin tantin nasu domin jin dumi.

Da Safiya kuma, an iske Mustafa da matarsa Amoun da ’yarsu mai shekara 12, Huda da jikarsu Hoor, mai shekara uku, a mace, sakamakon shakar iska mai guba.

Kamar yadda Nizar Hamadi, wanda dan uwan Mustafa ne ya bayyana, marigayin ya aika masa da sakon waya a daren da lamarin ya faru, inda ciki ya gaya masa cewa tantinsu wanda aka gina shi da bututun karfe da  tampol ya kasance marar kafar samun iskar shaka kuma kusan ba ya iya kare Mustafa da iyalansa daga tsananin sanyi.

“Lallai sanyin ya kai mizanin kasa da maki daya a ma’aunin Celsius (15.8 Fahrenheit) a wannan daren” kamar yadda Nizar ya fada wa Al Jazeera. “Dan uwana ba ya da wani zabi illa ya shigar da tukunyar gas cikin tantin da ke rufe ruf, babu mafitar iska, shin yana da wani zabi ne koma da bayan haka?”

Jarirai na daskarewa

Mata da yara kanana wadanda su ne kashi 80 cikin 100 na sababbin mutanen da suka rasa matsugunansu, su ne wadanda suka fi dandana kudarsu a lamarin.

Da yake bayyana halin da ake ciki a Syria a matsayin “mai matukar tada hankali,” Mark Lowcock, Shugaban Ayyukan Jinkai da Agajin Gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce, wadanda suka rasa muhallansu “na cikin mummunan kunci” kuma “an tilasta musu kwana a filin Allah a yanayin sanyin da ke daskarar da mutane sakamakon yadda sansanonin agaji suka cika suka batse.

“Iyaye kan kona robobi domin yaransu su ji dumi. Yayin da jarirai da kananan yara suke mutuwa sakamakon matsanancin sanyin,” inji shi.

A Sansanin Kalbeet a kwanakin baya, wata jaririya ’yar wata biyar mai suna, Areej Majid al-Hmeidi ta daskare inda ta rasu, kamar yadda Abu Anwar, wanda jami’i ne kuma mazaunin daya daga cikin sansanonin da ke kan iyakar Syria da Turkiyya.

Da yake magana da kafar labarai ta Al Jazeera, Anwar ya ce iyayen jaririya Areej ba sa son magana da kafofin labarai game da batun saboda “Suna zargin kansu kan yadda suka gaza wajen kare ta daga tsananin sanyin da ya daskarar da ita,” inji shi.

Yanayin da ake ciki a nan “ya yi munin gaske,” inji shi.

“Mutane na kona duk wani tarkace kawai domin samun dumi a jikinsu,” inji Anwar. “Akwai iyalai 800 a nan, ko kuma kimanin mutum 5,500, kuma kungiya daya ce kawai ke aikin agaji a nan, inda take samar mana da ruwa,” inji shi.