✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

SWAN ta yi taro don faxakar da masu horar da ’yan wasa

kungiyar Marubuta Labarin Wasanni Ta kasa reshen Jihar Kano (SWAN) ta gudanar da taron kara wa juna sani ga masu horar da ’yan wasa na…

kungiyar Marubuta Labarin Wasanni Ta kasa reshen Jihar Kano (SWAN) ta gudanar da taron kara wa juna sani ga masu horar da ’yan wasa na jihar don tunkarar wasannin kwallon kafa  na Tofa Frimiya da gwamnatin Jihar Kano ke xaukar nauyinsa wanda kuma za a fara a mako mai zuwa.

Da yake yi wa manema labarai karin haske game da taron  Shugaban kungiyar SWAN Rilwanu Idris Malikawa Garu ya bayyana cewa makasudin shirya taron shi ne don faxakar da masu horar da ‘yan wasa  a faxin jihar  game da kalubalen da ke gabansu na tunkarar wasannin da za a fara na Tofa firimiya, inda ya yi fata mahalarta taron za su yi amfani da abin da suka ji a wajen taron.

Da yake jawabi a wajen taron Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima ya yi kira ga masu horar da ’yan wasan da su tashi tsaye wajen neman ilimi, kasancewar sai mutum yana da abu kafin ya bayar da shi.  “Har kullum shi mai horar da ‘yan wasa malami ne don haka akwai bukatar ya koyar da ’yan wasansa komai da komai da ya shafi harkar wasanni, hakan ko ba za ta yiyu ba sai shi ma yana da cikkaken sani a wannan bangaren. Don haka akwai bukatar masu horar da wasanni su nemi ilimin abin lokaci bai kure ba kuma ba a giama da neman ilimi.”

A nasa jawabin Mataimakin Mai horar da kungiyar ‘Yan wasan kwallaon kafa ta kasa (Super Eagles Koc Salisu Yusuf ya ja hankalin masu horar da ‘yan wasan da su fi mayar da hankali wajen koyar da wasan fiye da koya musu motsa jiki. “mun sani cewa motsa jiki yana da muhimmanci ga xan wasa amma kada ya zama shi ne yake da kaso mafi yawa. Idan son samu ne kashi 80 na lokacin ya tafi a wajen horar da ‘yan wasa wasan kansa, sannan ragowar kashi 20 ya tafi wajen koyar da su guje-guje da sauransu. 

Da yake tofa albakacin bakinsa Shugaban  Hukumar Wasan kwallon kafa ta Jihar Kano Alhaji Sharif Rabi’u Ahlan ya nemi masu horar da ’yan wasan da su bi ka’idoji wajen kafa kungiyarsu tare da rikon amana wajen gudanaar da ayyukansu. 

Aminya ta rawaito cewa fiye da masu horar da yan wasa 60 ne da ke jihar suka halarci taron inda  a karshe aka rarraba musu shaidar halartar taron.

Sa’ad Alin Muazu wanda aka fi sani Koc Amo da yake shugabantar kulob xin Kano Life ya  yaba wa kungiyar SWAN bisa wannan taro da ta shirya, kasancewar inji shi ya karu da abubuwa da dama da suka shafi harkar kwallon kafa inda ya yi fatan za a ci gaba da shirya tarurukka irin waxannan don ci gaban harkar wasanni a Jihar Kano.