✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

SWAN ta nada kwamitin da zai gudanar da zabe a Kalaba

kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa reshen Jihar Kuros Riba  SWAN  ta nada kwamitin mutum uku da zai gudanar da zaben sababbin shugabannin kungiyar. Matakin…

kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa reshen Jihar Kuros Riba  SWAN  ta nada kwamitin mutum uku da zai gudanar da zaben sababbin shugabannin kungiyar.

Matakin ya biyo bayan taro da kungiyar ta saba yi ne a harabar filin wasa na U.J Esuene kuma an dora  masa  alhakin shiryawa da kuma  gudanar da tsabtataccen zabe.  An bai wa kwamitin mako biyu ya shirya tare da gudanar da tsabtataccen  zaben.

Wadanda aka nada su ne Kwamared bitalis Ugoh, na jaridar New Nigeria a matsayin shugaba, sai Eme Offiong, wakiliyar gidan radiyon Muryar Nijeriya (bON) da  Musa Kutama na jaridar Aminiya .

 Da yake nada kwmaitin, shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa reshen Kuros Riba Kwamared Albert Andinam, ya ce an ba su wa’adin makonni biyu kacal su shirya zaben sababbin shugabannin kungiyar ba tare dawani jinkiri ba.

Kamata ya yi a ce an gudanar da zaben shugabannin kungiyar tun cikin watan jiya (Oktoba) to amma saboda mutuwar Mataimakin shugaban kungiyar SWAN ta kasa shiyyar  Kudu maso Kudu Eddy Bekom ya sa aka dage zaben sai a wannan lokaci ne aka kafa kwmaitin da zai gudanar da shi.

Haka nan an amince a taron cewa Kwamared  Charles Eniang mawallafin jaridar Glimmer ya  maye gurbin da marigayi Eddy Bekom ya bari a kungiyar SWAN domin ya karasa wa’adin da ya bari. 

 Jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba ne ke da alhakin fitar da wanda zai maye gurbin sai dai an lura marigayin dan Kuros Riba ne da ke wakiltar jihohin biyu inda aka nuna Eniang ya maye gurbinsa duk da  Jihar Akwa Ibom za ta so a ce wani ne daga jihar ya maye gurbin marigayin tun da Jihar na daga cikin jihohi 6 da suka fito daga yankin Kudu maso Kudu da ake wakilta a kungiyar ta kasa.