A makon da ya arce, Jaridar Wirkililin taronsu, ta ranar karamin lauje da karamin lauje g watan Farin-biri na shekara ta dubu karamin luaje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, ta ruwaito yadda Gwamna Gwaramgwam Susun-wawan-Makurda ya kai tsegumin fullo a fadar bila da ke Tsaunin Aso, inda yak etas kulle-kullen ganin a kori Fullo daga makekiyar makiyayarsu da ke Harubja da Jihohin Kududdufi da Nasara, wai don kada su kaddamar da hare-hare a kan masu sana’ar na-dduke.
Susun-wawan-Makurda, Gwamnan Jihar Bini-ina-wai, ya yi ganawar sirri da Shugaba Jatau Mai-sa-in-sa da Haurobiyawa, ya jadadda muguwar manufarsa ta ganin ko ta halin kaka sai an kori Fuillo daga kasar Haurobiya. Watakila kuma so yake yi ya tattare musu turakun nagge, don ya nannage dadin nama, ko kuma tunda shi sana’ar na-duke al’ummarsa ke yi, shi yasa yake yunkurin kwace wa Fullo nagge, ya tura garke guda su rika yi masa huda. To ko ma dai da wacce irin manufa wannan susun ke son korar wadannan ’yan kasa daga kasarsu ta haihuwa, ya sani babu nasara.
Batu na ingarman karfn karafa, Susun-wawan-Makurda na matukar nuna gaba da kiyayya ga Fullo da Hausan-kejo, musamman ma domin mafi yawansu masu fuskantar alkibla ne don kadaita Mahalicci da ibada. Tunda in har ba a ari faden Malam Mantau ba, Lokacin da Gwamnan Jihar Tarba-tarba ya yiwo alkafura daga tsuntsun sama, kafafen yada labarai sun ruwaito yadda Susun-wawan-Makurda ya garzaya dakin addu’a da gicciye ya ce lallai a taimaka masa da rokon Mai-duka, domin su karamin lauje kawai suka rage a Arewacin Haurobiya, har ma ya yi nuni da cewa makirci aka kulla wa tsohon Gwamnan Bayan Kada, har aka halaka shi. Wannan mugun daji ya dade yana ruru wutar rikice-rikice a kasar nan. Idan har Shugaba Jatau ya bari ya auka tarkon Susun-wawan-Makurda, to za su bace-bat a dama-dama-dakurda-kurdar siyasar Haurobiya. Domin wannan mugun dajin babu abin da yake kitsawa sai shirin tada zaune tsaye.
Lallai masu yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, sun ce Sauna kira mana shasha, idan ka ga sakarai ku taho tare.’ Susu fullo ya fi karfinka, kuma ina tabbatar maka ‘hande on bone.’ Wanda duk ya ki ji, ba ya ki gani ba. Idan har kana shakkar abin da makarantarmu ke shirin nusar da kai ne, to ka tuntubi Di-Jango na Filfilon-toto ka ji yadda ya kwashe a karon battar da suka yi da Fullo, a lokacin da ya zuga ’yan Barema suka auka wa ’Yan Fullo, suka kwashe musu garken nagge, suka je suka nannagi dadin nama, amma karshen magijin babu wanda ya ji da dadi.
Haurobiyawa lokaci ya yi da za ku caccaki Susun-wawan-Makurda, domin yana son haifar muku da karancin nama, ya kuma haifar da yamutsi a tsakanin al’umma. Idan har Shugaba ne nagari, ya kamata a ce ya nusar da Gwamnatin Tarairayar Haurobiyawa kan yadda za ta mayar da garken naggen Fullo ya zama tamkar makekiyar makiyayar Arewacin Turai da ke kasar Danniyar-maki, kasar da ke samar wa nahiyar Turai a wasu sassan duniya naman nagge da kindirimo.
Kiwon nagge na cikin ayyukan da ke bunkasa tattalin dukiyar al’umma a nahioyoyin duniya, to ko me ya sa Susun-wawan-Makurda ke kokarin cutar da ’yan Fullo? Duk da cewa makarantarmu ba ta amince a biye wa wannan susun ba, amma ya kamata a yaga masa cuna, sannan ’yan Fullo su kwashe ina su, ina su, su arce zuwa Futa djallon da Futa-toro, ta yadda farashin nama zai kara tsula tsada, har ma a rika kiran sa da sunan tsada; kindirimo kuwa, sai ya zamto sai dan wane da wane. Kai ni dai Malam Dodo na yi tofin tsinuwa da tur da Susun-wawan-Makurda.
Gwamna Mai Sunan Sulalla na Jihar Jijjiga-ciyawa da Baba mai mangwaro ku ’ya’yan Fullo ne; Gwamna Mai Kwarankwatsin-tsiya na Birnin dabo kai dan Fullon Hausan-kejo ne; ina fatan kun ji bukatar da Susun-wawan-Makurda ya gabatar wa Fadar Shugaban kasar Haurobiya? To kalubalenku, tare da daukacin gungun gwamnonin arewazcin Haurobiya.
Kuma ina kira da karajin murya, kan lallai kungiyar ’ya’yan Fullo ta fito ta mayar wa Susun-wawan-Makurda, in ta kama ta gurfanar da shi a gaban kuliya manta sabo, domin ya yi musu zuki-ta-malle kama kare ka hada shi da zomo. Don haka a matsayina na Babban Direban allin wannan farfajiya, ina ganin wajibi ne Arewatawa su dauki amtaki kan Susun-wawan-Makurda, don so yake yi, tunda ana azabtar da al’ummar jihohin su Alan-guburo, sai kuma a auka wa jihohin Fullo da Hausan-kejo. Da yardar Mai-duka bakar aniyar Susun-wawan-Makurda za ta bishi.
Muna fatan Haurobiyawa sun fasko jirgin masu wsace wa fullo nagge, tare da kaddamar masa da hare-hare a rugarsa.
Susun-wawan-Makurda
A makon da ya arce, Jaridar Wirkililin taronsu, ta ranar karamin lauje da karamin lauje g watan Farin-biri na shekara ta dubu karamin luaje da…