Aminiya ta samo muku sunayen dalibai da malamai da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da su zuwa inda ba a sani ba daga makarantar Gwamnatin Tarayya da ke garin Kagara a Jihar Neja.
Da tsakar daren Laraba maharan suka bi gidajen malamai da sauran ma’aikata sannan suka ritsa dalibai a dakin kwanansu suka tisa keyar mutum 42 suka kuma kashe wani dalibi da ya nemi tserewa.
Mutanen da aka sace sun hada ds dalibai 27, malamai 3, sauran ma’aikata 3 da kuma iyalansu mutum tara.
Garin sunayensu da Aminiya ta samo:
Dalibai
- Jamilu Isah
- Shem Joshua
- Abbas Abdullahi
- Isah Abdullahi
- Ezekeil Danladi
- Haliru Shuaibu
- Mamuda suleman
- Danzakar Dauda
- Abdulsamad Sanusi
- Bashir Abbas
- Suleman Lawal
- Abdullahi Adamu
- Habakuk Augustine
- Idris Mohammed
- Musa Adamu
- Abdulkarim Abdulrahman
- Abubakar Danjuma
- Abdullahi Abubakar
- Bashir Kamalideen
- Mohammed Salisu
- Yusuf Kabir
- Isah Makusidi
- Plineous Vicente
- Lawal Bello
- Mohammed Shehu
- Mubarak Sidi
- Abdulsamad Nuhu
Malamai
- Hannatu Philip
- Lawal Abdullahi
- Dodo Fodio
Sauran ma’aikata
- Mohammed Musa
- Faiza Mohammed.
Iyalan ma’aikata
- Christiana Adama
- Faith Adama
- Maimuna suleman
- Nura isah
- Ahmad Isah
- Khadizat Isah
- Mohammed Mohammed
- Aisha Isah
- Saratu Isah
Tuni Shugaba Buhari ya umarci hukumomin tsaro su gaggauta kubutar da mutane da aka yi garkuwar da su.
Garkuwa da mutane masu yawa a lokaci guda na karuwa a Najeriya inda a yanzu Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Neja ke amfani da masu shiga tsakani wajen tattaunawa da maharan su sako mutanen da suka sace a Makarantar Sakandaren Kagara.