Gwamnatin tarayya ta ce jerin sunayen wadanda za ta ba lambar girmamawa ta kasa da ake ta yadawa a kafofin yada labarai na bogi ne.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Darkta Mai Kula da Hulda da ‘yan jaridu na Ma’aikatar kula da Ayyuka na Musamman, da kulla alaka tsakanin gwamnati da gwamnati, Julie Jacobs ta sa hannnu.
- Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
- Kamfanin Media Trust ya samu lambar yabo daga Hukumar NACA
Sanarwar ta tabbatar da labarin cewa, lallai shugaban kasa zai karrama wasu ’yan Najeriya da kuma masoya kasar da lambar girmamawa ta kasa.
Kuma za a yi bikin ne a ranar 11 ga watan Oktoba 2022, amma ba a fitar da jerin sunayen wadanda za a ba lambobin ba a hukumance.
“Muna kira ga jama’a da su yi watsi da jerin sunayen da ake yadawa, wannan ba komai ba ne illa aikin ’yan rige-rigen labarai ko da na karya ne,” a cewar sanarwar.
A jerin sunaen da ake yadawa; Shugaba Buhari zai bayar lambobin girmamawa ne ga sama da mutane 436 wadanda su ka yi abin a yaba a kasar.
Baya ga fitattun ’yan Najeriya, a cikin jerin sunayen da aka fitar da sanarwar ta karyata, har da Likitan Buhari, da surukinsa, da kuma wani hadiminsa Sabiu Tunde, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce.