✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

……Sun kwakule wa matar aure ido bayan sun yi mata fyade

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi na tuhumar wadansu mutane uku da ke kauyen Lukshi a karamar Hukumar Dass da laifin cire idon wata matar aure…

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi na tuhumar wadansu mutane uku da ke kauyen Lukshi a karamar Hukumar Dass da laifin cire idon wata matar aure mai suna Zainab Muhammad, bayan sun yi mata fyade a yayin da take kan hanyarta ta komawa gida daga wajen wani bikin nadin sarauta.
Wadanda ake zargin, Bitrus Yakubu Japan  da Sabo Rabo Katanga da Muhammad Sani da Bamigboye, wadanda suke zaune a kauyukan Durr da Dado, sun aikata wannan mugun aiki ne a ranar Asabar ta makon jiya da misalin karfe 11.30 na dare, bayan  Zainab ta bar wajen taron nadin sarautar Gimbiyar Lukshi ta nufi gida, sai wadanda ake tuhumar suka tare ta suka yi mata fyade kuma suka cire mata ido guda, sannan suka lahanta dayan.
daya daga cikin wadanda suka aikata laifin mai suna Bitrus, dan shekara 45, ya ce wani mutum mai suna Galambi ne ya sanya su cire mata idon don ya ba su naira miliyan daya. Game da aikata fyade kuwa, cewa ya yi jaraba ce ta sanya su yin hakan saboda dukkansu babu wanda yake da mata a cikinsu, kuma suna fama da talauci, ya ce wanda ya sanya su aikata wannan aiki bai ba su ko kwabo ba, ya ce sai ya gama amfani da idon ya hada layar bata kafin ya  biya su. An bi su har garinsu Dado  ne aka kama su.
Ya ci gaba da cewa, sauran mutanen, watau Sabo Rabo da Sani Bamigboye dukkansu sun yi amfani da ita bayan sun ba ta Naira dari, daga bisani kuma sai suka cire mata idon, ba tare da wani bata lokaci ba. Sun ce wannan shi ne na farko da suka taba aikata wannan mummunan aikin.
Sai dai kuma shi Galambi da suka ce shi ne ya sanya su aikata wannan aiki, da yake jawabi ga manema labarai ya ce shi bai sanya su  aikata wannan aiki ba, amma sun kawo masa ido ne suka ce ya hada musu layar bata a matsayinsa na wanda ya ce yana wannan aiki na hada layar bata.
Ita kuwa Zainab Muhammad da take bayanin yadda abin ya faru a yayin da take kwance a kan gadon asibitin koyarwa na jami’ar  Bauchi, ta ce ta fito ne daga wajen bikin nadin sarautar Gimbiya a Lukshi, sai mutanen suka kira ta suka bukaci aikata lalata da ita da cewa za su biya ta,  sai ta ce ba ta irin wannan aikin, bayanin da ta yi musu ya fusata su, daga nan sai suka kama ta suka kayar a kasa, suka yi mata fyade, bayan kowa ya gama sai kuma suka cire mata ido, guda dayan kuma da bai fita ba sai suka lalata shi.
Ta ce tana da aure da yara hudu, shi ne dalilin da ya sa ta bar wajen bikin ganin dare ya yi domin ta koma ga iyalanta. Ta koka game da zafin da yake damunta saboda idon da aka cire mata da kuma wanda aka lahanta.
Shi ma mahaifin Zainab mai suna Kwaya Wakili,  cewa ya yi yana gida ya samu labarin an kwakule idon ’yarsa,  sai aka tura su asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi, amma har ya zuwa wannan lokaci ba wani tallafi da suka samu, kuma wannan jinya ta fi karfinsa, saboda yana da yara biyar ga kuma rashin kudi da ake fama da shi a wannan lokaci, wannan mata kuma ita ce ’yarsa ta biyu. Don haka ya nemi taimakon gwamnati tare kuma da rokon a bi mata hakkinta wajen ganin an hukunta wadanda suka aikata mata wannan aiki, su ma a cire musu nasu idanun.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi, DSP Haruna Muhammad, wanda ya nuna masu laifin ga manema labarai, ya bayyana cewa suna ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da su a kotu domin fuskantar hukuncin da ya dace da su.