✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sun koma bautar gumaka don neman kariya daga kamuwa da Coronavirus

Addu’o’in ’yan kauyen na Shuklapur basu wani karbu ba sosai.

Wadansu mazauna kauyukan Indiya sun gina wurin bautar gumaka don neman su kare su daga kamuwa daga annobar Coronavirus.

Mutanen suna gabatar da addu’o’insu ga gumakan da fatar cewa za su shiga tsakaninsu da annobar, kuma za su iya kawar da annobar mai saurin kisa.

Masu bautar gumakan a kauyen Shuklapur da ke Arewacin Jihar Uttar Pradesh, suna ta yin addu’o’i da amfani da ruwa mai tsarki da kuma kai furanni a wurin bautar gumaka masu launin rawaya mai haske, inda suka ajiye gunkinsu da suke kira da “Corona Mata”.

“Watakila tare da albarkar mazauna kauyen, a kauyenmu, kowa yana samun saukin kamuwa daga annobar,” wata mazauniyar kauyen wadda ta bayyana sunanta da Sangeeta, ta ce a ranar Juma’a.

Indiya ta yi fama da annobar Coronavirus a cikin watannin Afrilu da Mayu, amma akwai alamun mafi munin abin zai iya wuce yadda ake tsammani.

Mahukunta sun bayar da rahoton cewa sababbin mutanen da suka kamu da cutar sun kai mutum dabu 84 da 332 a ranar Asabar 19 ga Yuni.

Alkaluman sun nuna cewa shi ne mafi karancin adadin da ake samu a kowace rana a sama da wata biyu, inji rahoton kididdigar ma’aikatar kiwon lafiya.

Kafar Labarai ta Reuters ta ruwaito cewa, addu’o’in ’yan kauyen na Shuklapur basu wani karbu ba sosai don har yanzu ana ci gaba da samun bullar annobar a cikin gundumar.

Sai dai kuma adadin masu kamuwa da ita ya yi kasa fiye da yadda yake a lokacin da ake fama da yaduwar annobar a kasar.